...Daga Bakin Mai Ita tare da Mudassir Haladu Dal

Bayanan bidiyo, Latsa lamar da ke sama domin kallo
...Daga Bakin Mai Ita tare da Mudassir Haladu Dal
An wallafa

A wannan makon za mu kawo muku fitaccen mai barkwancin nan a Kannywood wato Mudassir Haladu Dal a filin ...Daga Bakin Mia Ita .

Mudassir wanda haifaffen birnin Kano ne ya ce ba shi da uban gida a masana'antar Kannywood.

Sai dai kuma ya ce yana da jarumin da ya kasance tamkar madubu a wurinsa - "Ali Nuhu ne yake burge ni saboda ina zama na kalli fim dinsa. Sai kuma Umar Malumfashi wanda ya rasu. Ina son fina-finansu saboda idan ina kallo sai na ga kamar gaske."

Mudassir ya ce shi mutum ne mai son yin aktin "wannan dalilin ne ya sa na zaɓi barkwanci a fitowar da nake yi. Kuma Alhamdu lillah, barkwanci ya yi min rana."

Ma'aikata:

Ɗaukar bidiyo: Umar Ladu

Tacewa: Umar Ladu