Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Khusanov da Man City ta dauka?
Manchester City ta amince za ta biya Lens £33.6m, domin ɗaukar mai tsaron baya, Abdukodir Khusanov.
Wata majiya ta ce cikin ƙunshin yarjejeniyar, ɗan wasan zai ke karbar karin ƙudin ladan wasa da wasu tsarabe-tsarabe.
Zai je Ingila a auna koshin lafiyarsa a Etihad kafin daga baya a sanar da kammala cinikin mai tsaron bayan.
Kociyan City, Pep Guardiola na fatan kara karfin ƙungiyar a kakar nan, bayan kalubalen da yake fuskanta, wanda yake na shida a teburin Premier League.
Kenan City mai rike da kofin tana da tazarar maki 12 tsakaninta da Liverpool, wadda ke jan ragama, mai kwantan wasa da Everton.
Khusanov zai zama na farko daga Uzbekistan da zai buga Premier League a tarihi - zai kuma zama na farko da City za ta ɗauka a Janairu tun bayan Aymeric Laporte a 2018.
Lens ta ɗauki Khusanov kan £84,000 daga Energetik-BGU ta Belgium kan yarjejeniyar wata 18 da ta wuce.
Daga nan ya sa ƙwazo, wanda yanzu ya yi wasa 13 a Ligue 1 a kakar nan, wanda ya buga wa tawagar Uzbekistan karawa 18.
Khusanov ya fara ci wa Lens ƙwallo a karon farko a French Cup a wasa da Paris St Germain ranar 22 ga watan Disamba.