Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matashin Tottenham Moore ya kafa tarihi a gasar zakarun Turai
Tottenham ta kai zagayen gaba kai tsaye a Europa League, bayan da ta doke Elfsborg 3-0 ranar Alhamis a wasan karshe a cikin rukuni.
Ƙungiyar da ke buga Premier League ta yi rashin ƴan wasa 12 da ke jinya da waɗanda ba su cancanta ba, sai Radu Dragusin ya ji rauni a zagaye na biyu, wanda ya shiga sauyi.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Tottenham ta fara cin ƙwallo ta hannun Dane Scarlett, sannan Damola Ajayi ya kara na biyu, sai Mikey Moore ya kara na uku daf a tashi.
Ƙwallon farko da matashin mai shekara 17 ya ci wa Tottenham, wanda ya kafa tarihi a gasar ta zakarun Turai.
Moore, wanda aka haifa a Landan mai shekara 17 da kwana 172 ya doke tarihin da Jimmy Greaves ya kafa mai shekara 17 da kwana 245 a Oktoban 1957 a matakin matashin da ya zura ƙwallo a raga a gasar ta zakarun Turai.
Tottenham ta kai zagayen gaba kai tsaye da maki 17 a mataki na huɗu, bayan cin wasa biyar da canjaras biyu aka doke ta karawa ɗaya.
Ranar Lahadi Tottenham za ta ziyarci Brentford, domin buga wasan mako na 24 a Premier League.