Alexander-Arnold na dab da komawa Real Madrid, Man City na zawarcin Ola Aina

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan baya na Liverpool Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, yana dab da ƙulla yarjejeniya da Real Madrid, yayin da ɗan wasan na Ingila ya ci gaba da yin watsi da sabbin tayin tsawaita kwantiraginsa da zai ƙare a bazara. (AS)

Liverpool za ta yi harin ɗan wasan baya na Bayer Leverkusen ɗan ƙasar Netherlands Jeremie Frimpong da ɗan wasan baya na Bayern Munich da Canada Alphonso Davies, idan Alexander-Arnold ya koma Real Madrid. (Teamtalk)

Manchester City na zawarcin dan wasan baya na Nottingham Forest da Najeriya Ola Aina, mai shekara 28, a matsayin wanda zai iya maye gurbin Kyle Walker ɗan ƙasar Ingila mai shekara 34. (Sun)

Arsenal na zawarcin golan Espanyol Joan Garcia, mai shekara 23, amma kulob ɗin na La Liga ya ci gaba da dagewa kan farashin fam miliyan 25. (Mirror)

Ɗan wasan gaban Portugal da Al-Nassr Cristiano Ronaldo, mai shekara 39, ya ƙi cire rai kan komawa Manchester City, duk da cewa ya buga wa abokiyar hamayyarta Manchester United. (Talksport)

Newcastle United tana zawarcin ɗan wasan bayan Lens Abdukodir Khusanov wanda ke da farashin fam miliyan 25, amma za ta fuskanci hamayya kan ɗan wasan na Uzbekistan, mai shekara 20, daga ƙungiyoyin Premier da suka haɗa da Manchester City da Tottenham Hotspur da Leicester City da kuma Wolves. (Chronicle)

Ɗan wasan baya na Crystal Palace Tyrick Mitchell, mai shekara 25, baya sha'awar ƙulla yarjejeniyar dogon zango a kulob ɗin na Landan, inda Atletico Madrid ke zawarcin ɗan wasan na Ingila. (Caught Offside)

Da wuya Manchester City za ta ci gaba da zawarcin ɗan wasan tsakiya na Sifaniya Martin Zubimendi, mai shekara 25, wanda har yanzu ba ya sha'awar komawa Ingila daga Real Sociedad. (TBR Football)

Southampton da Ipswich duk suna sha'awar ɗaukar ɗan wasan Rennes da Finland Glen Kamara, mai shekara 29 a watan Janairu. (TBR Football)

Real Betis na tattaunawa da wakilan ɗan wasan tsakiya na Brazil Arthur, mai shekara 28, kan kwantiragin aro daga Juventus. (Sport)

Brighton na shirin dawowa da mai tsaron gida Carl Rushworth, mai shekara 23, daga zaman aro da ya ke yi a Hull City, yayin da ƙungiyoyin Premier ke rububin ɗan wasan na Ingila. (Football Insider)