Arsenal ta ci gaba da matsar Liverpool a teburin Premier

Asalin hoton, Getty Images
Riccardo Calafiori ne ya ci wa Arsenal ƙwallon da ta doke Wolverhampton 1-0 a Premier League ranar Asabar a Molineux.
Gunners ta karasa fafatawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Myles Lewis-Skelly jan kati.
Mai shekara 18 da kwana 121 ya zama na uku matashi da aka kora a wasa a Premier League, bayan Wayne Rooney da kuma Michael Owen.
Haka itama Wolves an korar mata Joao Gomes, bayan da ya karɓi katin gargaɗi na biyu, sakamakon ketar da ya yi wa Jurrien Timber, saura minti 20 a tashi karawar.
Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta biyu a teburi Premier da maki 47 bayan wasannnin mako na 23.
Liverpool mai kwantan wasa da Everton, ita ce ke kan gaba da maki 57, wadda ta ci karawa 16, wasa ɗaya ne ta yi rashin nasara a bana, shi ne a hannun Nottingham Forest.
Ranar Laraba 29 ga watan Janairu, Arsenal za ta je Girona, domin buga wasan karshe a cikin rukuni a Champions League, Gunners tana mataki na uku.
Daga nan Arsenal za ta karɓi bakuncin Manchester City a gasar Premier League ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu a Emirates.










