Chelsea ta kammala ɗaukar Felix daga Atletico ta bayar da Gallagher

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta kammala cinikin ɗan wasan tawagar Portugal, Joao Felix daga Atletico Madrid kan £45m ta yi musaya da ɗan wasan Ingila, Conor Gallagher kan £33m.

Felix, mai shekara 24, wanda ya amince da yarjejeniyar shekara bakwai zai sake komawa Chelsea, bayan da ya ci ƙwallo huɗu a wasannin aro 20 da ya yi mata a 2023.

Shi kuwa Gallagher ya saka hannu kan ƙunshin ƙwantiragin kaka biyar a ƙungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Gallagher ya fara Chelsea daga makarantar horar da tamaular ƙungiyar tun yana da shekara shida - ya ci wa Chelsea ƙwallo 10 a karawa 90 da ya yi wa babbar ƙungiyar.

Ɗan wasan ya shiga kakar karshe ta yarjejeniyarsa a Stamford Bridge, kenan Chelsea ta sayar da shi maimakon ta yi hasara, idan an kammala kakar bana.

Bayan da Chelsea ta ci karo da tsaiko kan cinikin Samu Omorodion daga Atletico, hakan ya sa Gallagher bai kammala komawa Sifaniya ba, bayan da Atletico ke neman ƙudin da za ta ɗauki ɗan wasan.

Gallagher ya yi kwana biyar a otal a Madrid a farkon watan nan, bayan da ake sa ran za a kammala ƙulla yarjejeniya tsakanin ƙungiyoyin biyu.

Ɗan wasan tawagar Ingila ya buga wasannin aro a Charlton da Swansea da West Brom da kuma Crystal Palace daga nan ya koma ƙungiyarsa Chelsea a 2022-23.

Ya buga wa Ingila wasa 18 tun da ya fara taka mata leda a 2021, yana cikin waɗanda suka buga wa tawagar gasar kofin duniya a Qatar a 2022 da Euro 2024.