Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United za ta ziyarci Spurs a Carabao
Manchester United za ta je gidan Tottenham a wasan kusa da daf da na ƙarshe a kofin Carabao.
Masu riƙe da kofin Liverpool za su zaiyarci Southampton da ke ta fama a gasar Premier.
A wasan hamayya na Landan Arsenal za ta karɓi baƙunci Crystal Palace, yayin da Newcastle za ta fafata da Brentford a gida.
Za a yi wasannin kusa da daf da na ƙarshen ne a satin 16 ga watan Disambar wannan shekarar.
Wannan ne karo na farko cikin shekara 14 da za a yi wasan ba tare da kungiyoyin gasar Championship ba.
Tottenham ta doke City a zagaye na huɗu na gasar.
United da ta casa Leicester City 5-2 ƙarƙashin kocin riƙon kwarya Ruud Van Nistelrooy - na fatan kawo Ruben Amorim a matsyin kocinta nan gaba.
Za a buga wasannin kusa da na ƙarshe ne a tsakanin 6 ga watan Janairu da 3 ga watan Fabirariru, a buga wasan ƙarshe a Wembley a ranar 16 ga watan Maris.
Wasannin kusa da na ƙarshe:
Tottenham v Manchester United
Arsenal v Crystal Palace
Newcastle v Brentford
Southampton v Liverpool