Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jamus tana da jan aiki kafin Euro 2024 - Hamann
Tawagar kwallon kafa ta Jamus tana da jan aiki a gabanta idan har tana son taka rawar gani a gasar cin kofin nahiyar Turai a 2024, in ji Dietmar Hamann.
Jamus, wadda za ta karbi bakuncin wasannin za ta fara wasan farko da Scotland, wanda shi ne labulen bude gasar ranar 14 ga watan Yuni.
Jamus, wadda za ta yi wasanninta a Munich tana rukunin farko da ya kunshi Hungary da kuma Switzerland.
Hamann tsohon dan wasan tawagar Jamus, wadda ya yi wa wasa 59 tsawon shekara takwas, ya buga tamaula a kungiyoyin Ingila.
Kamar yadda ya sanar da BBC ya ce ''A gasar kofin duniya biyu da aka buga, an fitar da Jamus a karawar cikin rukuni.''
''Muna da babbar matsala. An doke mu wasa da yawa a 2023 fiye da waɗanda muka yi nasara.
Mun yi rashin nasara a hannun Poland da Belgium da Turkiya da Austria, muna da tarin matsaloli.''
Tun bayan da Jamus ta kori, Hansi Flick, ta maye gurbin sa da tsohon kocin Bayern Munich, Julian Nagelsmann a cikin watan Satumba.
Ya zama matashi na biyu da aka bai wa aikin kociyan tawagar Jamus mai shekara 34, wanda ke aikin rikon kwarya zuwa bayan gasar Euro 2024.