Tserewar Falasɗinawa zuwa Masar da gasar kamun Kifi cikin hotunan Afirka

An wallafa

Ƙayatattaun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya

.

Asalin hoton, KHALED DESOUKI/AFP

Bayanan hoto, An baje kolin irin ayyukan zayyana na Rashid al-Khalifa a Kasar Masar.
.

Asalin hoton, BRIAN INGANGA/REUTERS

Bayanan hoto, Sojojin Kenya sun gudanar da fareti yayin ziyarar Sarki Charles na Ingila ranar Alhamis, bayan ya roki a yafewa Ingila azabar da ta 'dan'danawa Mau Mau masu adawa da mulkin mallaka shekaru 70 da suka gabata.
.

Asalin hoton, BENSON IBEABUCHI/AFP

Bayanan hoto, Masu sanya kayan 'kawa sun yi nunin rigunan Bubu Ogisi ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO/AFP

Bayanan hoto, A Abidjan ranar Saint's Day Roukiata Ouédraogo ta na gabatar da sabin wakoki.
.

Asalin hoton, MOHAMMED ABED/AFP

Bayanan hoto, Falasdinawa sun tsallaka Masar bayan an sake bude iyakokin Rafah, don tserewa rikici.
.

Asalin hoton, FAYEZ NURELDINE/AFP

Bayanan hoto, Francis Ngannou 'dan damben Kamaru ya kaiwa Tyson Fury na Burtaniya duka ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, LOU BENOIST/AFP

Bayanan hoto, Yayin gwanjon agoguna da lambobin girmamawa na shugaban kasar Sinigal na farko Léopold Sédar Senghor ranar Juma'a a Faransa.
.

Asalin hoton, JEROME FAVRE/EPA

Bayanan hoto, A ranar kuma an gudanar da gasar kamun kifi a birnin Saint Louis dake Arewacin Sinigal.
.

Asalin hoton, ANNE-CHRISTINE POUJOULAT/AFP

Bayanan hoto, Da yammacin ranar a Faransa, Kaftin Siya Kolisi ya sumbaci kofin gasar wasan zari-ruga na duniya bayan ya jagoranci Afirka ta Kudu ta yi nasara har sau hudu.