Europa League: Liverpool za ta fafata da Atalanta

An wallafa

Liverpool za ta kece raini da Atalanta a wasan zagayen kwata fainal na gasar Europa a yayin da AC Milan za ta fafata da Roma.

Za a yi karawar farko a ranar 11 ga watan Afrilu inda karawa ta biyu kuma za a yi a ranar 18 ga watan na Afrilu.

A ranar 2 ga watan Mayu za a buga wasan zagayen kusa da ƙarshe, sai kuma wasa na biyu na zagayen kusa da ƙarshe a ranar 9 ga watan Mayu.

Jadawalin

Zagayen kwata fainal

  • AC Milan v Roma
  • Liverpool v Atalanta
  • Bayer Leverkusen v West Ham
  • Benfica v Marseille

Zagayen kusa da ƙarshe

  • Benfica ko Marseille v Liverpool ko Atalanta
  • AC Milan ko Roma v Bayer Leverkusen ko West Ham