Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abinda kuke son sani kan wasan Atletico da Barcelona
Atletico Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na 29 a gasar La Liga da za su fafata ranar Lahadi a Metropolitano.
Sun kara a wasan farko a bana ranar 3 ga watan Disambar 2023, inda Barca ta ci 1-0 ta hannun Joao Felix.
Real Madrid ce ta daya a teburin La Liga da maki 72, sai Girona mai maki 62 da kuma Barcelona ta uku da maki 61.
Atletico Madrid ce ta biyar da maki 55 da tazarar maki daya tsakaninta da Bilbao ta hudun teburin.
Wasa tsakanin Atletico da Barcelona yana da girma, kuma kungiyoyin biyu suna cikin wadanda suka kai kwata fainals a Champions League na bana.
Barcelona ta kai matakin daf da na kusa da na karshe, bayan nasara a kan Napoli, ita kuwa Atletico ta yi waje da Inter Milan.
Barca mai rike da kofin bara na La Liga ta hada maki 17 daga 21 da ya kamata ta samu, kenan tana komawa kan ganiya.
To sai dai Barcelona na kokarin ganin ta kara taka rawar gani a bana, to amma nasarar da Real Madrid ke samu da jan ragamar teburin La Liga abin da wuya.
Ranar Asabar Real Madrid ta je ta ci Osasuna 4-0 a wasan mako na 29 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Kenan fatan Barca shi ne rage tazarar makin da yake tsakaninta da Real Madrid, kuma idan har ta ci Atletico zai sa ta koma ta biyun teburi.
Filin wasa na Atletico da ake kira Metropolitano
Cin wasa a Civitas Metropolitano yana da dan karen wahala, musamman a kakar tamaula ta bana.
Atletico ta yi nasara a dukkan wasannin da ta buga a gida, in banda 3-3 da ta tashi da Getafe a lik.
A fafatawar da Atletico take yi a waje a bana nan ne take cin karo da koma baya, wadda maki biyu kacal ta hada daga wasa tara baya da ta kai ziyara har da wanda Cadiz ta doke ta a makon jiya.
Hakan ya sa tana ta biyar a kan teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Bilbao ta hudu a kokarin samun gurbin karshe a Champions League na badi.
To sai dai Barcelona ta kwan da cewar da zarar ta yi nasara a kan Atletico za ta koma ta biyun teburi, ita kuwa kungiyar da Diego Simone ke jan ragama za ta dare mataki na hudu da zarar ta doke ta Xavi.
Wadanda suka buga wa kungiyoyin tamaula
Wasu 'yan wasa da suka buga wa kungiyoyin biyu tamaula sun hada da Joao Felix tsohon dan kwallon Atletico, wanda yanzu ke Barcelona.
A wasan farko da suka kara a bana a Estadio Olimpi, shi ne ya ci wa Barca kwallon da ta yi nasara 1-0 a kan Atletico.
Haka kuma Atletico tana da wani dan kwallon mai hatsari, Antoine Griezmann da kuma Memphis Depay, wadanda ke kan ganiya a kakar nan.
Wasu labaran da suka shafi kungiyoyin biyu.
Frenkie de Jong da Pedri da Gavi da kuma Alejandro Balde na jinya, sai dai Marcos Alonso da kuma Ferran Torres na murmurewa cikin sauri, wadanda watakila a bayyana su cikin wadanda za su buga karawar ta Lahadi.
Ita kuwa Atletico Madrid na auna koshin lafiyar Griezmann, wanda ke dauke da rauni, amma ya buga wa kungiyar Champions League ranar Laraba.
Sauran da ke jinya sun hada da Jose Gimenez da kuma Thomas Lemar, yayin da ake auna koshin lafiyar Mario Hermoso.