Ƴan Barcelona da za su karɓi bakuncin Sociedad a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona za ta kara da Real Sociedad a wasan mako na 35 a La Liga da za su kara ranar Litinin a Estadi Olímpic Lluís Companys.
Wannan shi ne karo na biyu da za su kara a tsakaninsu a bana, inda ranar 4 ga watan Nuwambar 2023 Barcelona ta je ta ci 1-0, kuma Ronald Araujo ne ya ci kwallon.
Barcelona ce ta ukun teburi da tazarar maki biyu tsakani da Girona ta biyu mai maki 75, ita kuwa Sociedad tana ta bakwai a teburi da maki 54.
Barcelona na fatan komawa mataki na biyu, domin ta samu damar buga Spanish Super Cup, bayan da kofin La Liga ya kuɓuce mata a bana.
Ana buga Spanish Super Cup ne tsakanin wadanda suka buga wasan karshe a Copa del Rey da wadda ta lashe La Liga da ta biyun teburin kakar.
A karshen mako Real Madrid ta yi bikin lashe kofin La Liga na bana na 36 jimilla, ita ce kan gaba a yawan daukar kofin.
Real Madrid za ta buga wasan karshe da Borussia Dortmund a Champions League ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.
Real tana da kofin zakarun Turai 14, ita kuwa Dortmund tana da daya, wadda karo na uku da za ta fafata a wasan karshe a gasar.
Tuni dai kociya, Xavi Hernandez ya bayyana ƴan wasan da za su fuskanci Sociedad a ranar ta Litinin.
Ƴan wasan Barcelona:
Ter Stegen, João Cancelo, R. Araujo, I. Martinez, Ferran, Pedri, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix da kuma Christensen.
Sauran sun hada da Fermín, Marcos A., Romeu, Vitor Roque, S. Roberto, Gündoğan, Kounde, Lamine Yamal, Kochen, Cubarsí da kuma H. Fort.









