Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Modric zai bar Real Madrid,Al-Ittihad na zawarcin Salah,Chelsea na son Osimhen
West Ham na zawarcin dan wasan gaban Bournemouth da Ingila Dominic Solanke mai shekara 26 (Telegraph - subscription required)
Chelsea ta sha gaban Arsenal a rige -rigen da suke yi don siyan dan wasan gaban Napoli da Najeriya, Victor Osimhen dan shekara 25 a wannan bazara . (Teamtalk)
Kocin Bayern Munich Thomas Tuchel zai koma Ingila bayan ya bar kungiyar ta kasar Jamus a karshen kakar wasanni (Telegraph - subscription required)
Jurgen Klopp ba zai maye gurbin Tuchel a Bayern Munich ba idan ya bar Anfield a karshen kakar wasanni a cewar wakilinsa (Sky Sports Germany - in German)
Dan wasan gaban AC Milan da Faransa Olivier Giroud mai shekara 37 watakila ya koma taka leda a MLS a karshen kakar wasanni. (Corriere dello Sport - in Italian)
Chelsea za ta saurari tayin da ake yi wa mai tsaron ragar Sfaniya Robert Sanchez mai shekara 26 a wannan bazara kuma watakila kungiyar ta maye gurbinsa a wannan bazara (Football Insider)
Sai dai kungiyar ta Chelsea ba ta za ta bada dan wasanta mai tsaron baya ba Levi Colwill dan shekara 20 wanda ke jan hankalin Paris St-Germain da Liverpool. (Standard)
Dan wasan tsakiya na Real Madrid da Croatia Luka Modric mai shekara 38 zai bar kungiyar a wannan bazara . (Bild - in German)
Al-Ittihad na son ta dauko dan wasan gaban Tottenham da Koriya da Kudu Son Heung-min mai shekara 31 da dan wasan gaban Liverpool da Masar Mohamed Salah mai shekara 31 a wannan bazara a kasuwar sayar da yan wasa . (Football Transfers)
Manchester United da Arsenal sha’awar dan wasan gaban Bayern Munich da Faransa, Mathys Tel dan shekara 18. (Bild - in German)
Tottenham da Newcastle na zawarcin dan wasan tsakiya na Everton James Garner mai shekara 22. (Football Insider)
Liverpool na son ta sayi dan wasan tsakiya na Brazil Luis Guilherme dan shekara 18 daga Palmeiras a wannan bazara. (Football Insider)
Chelsea da Arsenal su ne a gaba -gaba wajan dauko dan wasan tsakiyar baya na Aberdeen Lewis Carrol dan shekara 15 a karshen kakar wasanni . (The Athletic)