Mazan da ake haya a matsayin iyayen jabu don yin takardun ɗan ƙasa

An wallafa

Binciken BBC ya gano cewa mazaje a Birtaniya na karɓar maƙudan kuɗaɗe domin ƙaryar kasancewa mahaifan jariran da mata 'yan ci-rani suka je da cikinsu ƙasar.

Binciken ya nuna cewa mata 'yan ci-rani kan biya mazajen ƙasar fam 10,000, domin su sanya sunansu a takardar haihuwar jariran - lamarin da zai bai wa yaro damar zama ɗan ƙasa a Birtaniya, uwayen kuma su samu izinin zama.

Akwai 'yan damfara da dama da ke amfani da shafin Facebook suna iƙirarin cewa sun taimaki dubban mata, ta wannan wannan hanya.

To amma kamfanin Facebook ya ce ire-iren waɗannan abubuwa sun saɓa wa dokokinsa.

Binciken da BBC ta gudanar, ya gano cewa irin wannan zambar na faruwa a sassa daban-daban a Birtaniya.

Haka kuma binciken ya gano wakilan da ke aikin samar da iyayen ƙarya

Mai bincike ta yi fitar burtu a matsayin mai juna biyu da ta je Birtaniya ba bisa ƙa'ida, kuma take neman irin waɗannan mazaje, ta kuma samu damar yin magana da mazaje da dama da ke wannan sana'a.

Ɗaya daga cikin wakilan mai suna Thai, ya faɗa mata cewa yana da mazaje masu yawa da za su yi mata wannan aiki, na zama mahaifin bogi, amma ya ce za ta biya shi fam 11,000.

Ya bayyana matakan da ake bi wajen gudanar da wannan aiki a matsayin ''abu mai sauƙi'', ya kuma ce zai yi bakin ƙoƙarinsa wajen samar wa jaririn takardun zama ɗan Birtaniya.

Thai, wanda ba ya tallata sana'arsa a Facebook, ya ce akwai dabarun da yake bi don aiwatar da sana'ar tasa.

Ya gabatar da mai binciken ga wani ɗan Birtaniya da ake kira Andrew, wanda ya ce ya yarda zai zama mahaifin jaririn da ke cikinta, bisa alƙawarin za a biya shi fam 8,000.

A lokacin ganawarsa da wakiliyar BBC, Andrew ya nuna mata takardar shaidarsa ta zama ɗan Birtaniya.

BBC ba ta biya kuɗi ga kowanne wakili ba, da nufin samar mata wanda zai zama mahaifin ƙarya a yayin wannan bincike.

Wata wakiliyar da ke sana'ar samar da iyayen ƙarya ga masu juna biyu, da ake kira Thi Kim, ta yi iƙirarin cewar ta taimaka wa dubban mata.

Ta ce za ta samar da namijin da zai yi aikin, kuma za a biya dala 10,000 domin wannan aiki, tare da ladanta da ya kai dala 300.

Ana kallon yin ƙaryar zama mahaifi a matsayin babban laifi, kamar yadda lauyar hukumar shige-da-ficen Birtaniya, Ana Gonzalez ta bayyana.

Idan mace ta je Birtaniya ba bisa ƙa'ida ba, sannan ta haifi jariri da ɗan Birtaniya ko yake zaune a Birtaniya, to kai-tsaye jaririn ya zama ɗan Birtaniya.

Daga nan kuma mahaifiyar za ta iya neman takardar izinin zaman Birtaniya, lamarin da zai ba ta damar ci gaba da zama a ƙasar, sannu a hankali kuma ta nemi takardar shaida cikakkiyar 'yar ƙasa.

BBC ba za ta iya ƙiyasin girman wannan matsala ba, yayin da ofishin ma'aikatar cikin gida ta ƙasar ke cewa ba za ta iya fayyace adadin zargin da take yi a kan lamarin ba.

Ofishin ya kuma ce ba zai wallafa adadin takardun izinin zaman Birtaniya da ya bai wa iyayen da suka shiga ƙasar tare da haifar jarirai ba.

Ofishin ya shaida wa BBC akwai matakan da yake bi domin gano masu zambatar hukuma ta hanyar amfanin da takardun haihuwa na ƙarya domin samun izinin zama.

Binciken BBC ya gano cewa waɗannan haramtattun ayyuka, ana tallata su a wani zauren shafin Facebook da ake amfani da harshen Vietnam da ke neman ma'aikata.

'A Facebook ake tallata neman aikin'

Mun samu gomman saƙonni daga mutanen da ke cikin zauren, waɗanda suka haɗar da matan da ke neman wanda zai zame musu mahaifin jaririn da ke cikinsu, da kuma mazan da ke cewa a shirye suke su zama iyayen ƙarya.

Wata mata ta wallafa wani saƙo a zauren da ke cewa: ''Ina da ciki ɗan wata huɗu. Ina matuƙar neman uba ɗan ƙasa wanda shekarunsa suka kama daga 25 zuwa 45''.

Wani saƙon kuma ya ce: ''A shirye nake na zama uba, idan kina da ciki kuma baki samu wanda zai zame miki mijin ƙarya ba, ki tuntuɓe ni a asirce''.

Facebook ya ce ba zai bari a riƙa ɗaukar iyayen ƙarya ta hanyar amfani da shafinsa ba, ya alƙawarta ci gaba da cire saƙonnin da suka saɓa wa tsare-tsaren kamfanin.

'Sau uku muka haɗu da wanda ya zame min uban jariri'

Mun tattauna da wata mace da ta shaida mana cewa ta biya fam 9,000 ga wani mutum domin ya yarda ya zama uban ɗanta

Ta ce mutumin ya fi ta da shekara 30.

Na ma ji cewa ya taɓa yin wannan aiki ga wata matar.

Ta ce ba ta yi wata mu'amala mai yawa da mutumin ba.

A cewarta, sau uku kawai suka haɗu, ciki har da haɗuwar da suka yi lokacin da suka je ofishin rijistar haihuwa domin karɓo wa jaririn takardar haihuwa.

Wata mace daban, ta shaida mana cewa ta biya wani mutum fam 10,000 domin ya zame mata uban ƙarya ga jaririnta, daga baya kuma ta gano cewa ba shi da takardun izinin zama ɗan ƙasar.

Wani lauya mai suna Harjap Bhangal ya ce ya kamata ofishin ma'aikatar cikin gida ya riƙa bincike mai zurfi kafin bayar da takardun shaidar zama a Birtaniya.

''Idan aka zo da jaririn da aka haifa, kuma ɗaya daga cikin iyayensa ba shi da takardar zaman Birtaniya, to ya kamata a buƙaci gwajin ƙwayoyin halitta, daga yaron da kuma duka iyayen nasa'', in ji shi.

A Birtaniya dai ba a buƙatar gwajin ƙwayoyin halitta kafin yi wa yaro takardar haihuwa.