Banyana-Banyana ta doke Falcons a gasar kofin Afirka ta mata

An wallafa

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Afirka ta Kudu ta yi nasara a kan ta Najeriya da ci 2-1 a wasan farko a rukuni na uku a gasar cin kofin Afirka a Morocco.

Banyana-Banyana ta ci kwallayen ta hannun Jermaine Seoposenwe da kuma Hildah Tholakele Magaia.

Najeriya ta zare kwallo daya daf da za a tashi daga karawar ta hannun Rasheedat Ajibade.

Super Falcons mai kofi uku a jere 11 jumulla a gasar kofin Afirka, za ta yi wasa na biyu a rukuni na uku da Bostwana ranar 7 ga watan Yuni.

A kuma ranar Banyana-Banyana za ta kece raini da Burundi.

A cikin watan Satumba tawagar Afirka ta Kudu ta doke Super Falcons da ci 4-2 a gasar Aisha Buhari Cup ta kuma lashe kofin a Najeriya.

Ranar Talata Rukunin farko zai yi wasa na biyu, inda mai masaukin baki Morocco za ta fafata da Uganda, yayin da Senegal za ta yi gumurzu da Burkina Faso.

Morocco tana da maki uku, bayan cin Burkina Faso 1-0 ranar Asabar, ita kuwa Senegal ta doke Uganda 2-0 ranar Lahadi.