Nottingham Forest ta ɗauki Ola Aina

An wallafa

Nottingham Forest ta kammala ɗaukar ɗan kwallon tawagar Najeriya, Ola Aina daga Torino kan yarjejeniyar kaka ɗaya.

Mai tsaron bayan, mai shekara 26 ya koma buga gasar Serie A daga Chelsea a 2018, kuma shi ne na farko da Forest ta ɗauka a bana.

Haka kuma kungiyar ta kusan kammala cinikin ɗan wasan Manchester United, Anthony Elanga.

Steve Cooper kociyan Forest ya ce ''Aina yana da kwarewa a kan Premier League da Serie A, kenan gogaggen ɗan wasa ne.''

Mai tsaron bayan ya sake komawa buga Premier League a kakar 2020/21, bayan da ya kammala wasannin aro a Fulham.

Aina, wanda aka haifa a birnin Landan ya buga wa tawagar Ingila ta matasa wasa daga baya ya zaɓi ya yi wa Najeriya tamaula.

Ya fara yi wa Super Eagles tamaula a 2017, wanda kawo yanzu ya yi karawa 30 a tawagar ƙasar.