Ina aka kwana game da zaben gwamna a Adamawa da Abia da Kebbi da Enugu?

An wallafa

A ranar 18 ga watan Maris din 2023 ne a aka gudanar da zaben gwamna a wasu jihohin Najeriya.

An dai gudanar da zaben ne a jihohi 28 cikin 36 da ke Najeriyar. Zaben ya yi zafi a wasu jihohin kasar da har ta kai ga samun takaddama kafin a sanar da sakamakon zabensu.

Zuwa yanzu, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC ta bayyana sakamakon wasu jihohin inda Jam'iyyar APC ta lashe jihohi 15 sai kuma babbar jam'iyyar hamayyar kasar, PDP da ta samu nasara a jihohi takwas yayin da jam'iyyar NNPP ta samu jiha guda daya.

Sai dai zaben a wasu jihohi hudu - Adamawa da Abia da Kebbi da Enugu, ya bar baya da kura inda INEC ta dauki matsaya a kansu saboda takaddamar da ta biyo baya.

Bari mu yi duba kan abubuwan da suka faru a zaben da aka gudanar a wadannan jihohin.

Adamawa

Babban jami'in tattarawa da sanar da sakamakon zabe a jihar Adamawa ya bayyana zaben gwamna na jihar da aka yi ranar Asabar a matsayin wanda bai kammala ba.

Jami'in ya bayyana haka ne ranar Litinin a cibiyar tattara sakamakon zaben bayan da aka sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Fufore da ake ta dako.

Bayan sanar da sakamakon kananan hukumomi 21 na jihar, Ahmad Umar Fintiri na Jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 421,524.

Yayin da babbar abokiyar hamayyarsa ta Jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani ta samu kuri'u 390,275.

Sai dai baturen zaben ya ki amincewa da sakamakon zaben da aka kawo daga karamar hukumar Fufore inda ya ce an samu banbanci a alkaluman da aka sanar da kuma wanda aka dora a shafin hukumar zabe.

Duka jam'iyyun dai sun kalubalanci matakin da baturen zaben ya dauka inda kowane bangare ke ikirarin shi ya yi nasara a zaben.

Zaben da aka yi a jihar na daya daga cikin wadanda hankali ya karkata a kai la'akari da cewa wannan ne karon farko da aka samu mace daga arewacin Najeriya da ta tsaya takarar gwamna a jihar Adamawa.

Abia

Kakakin hukumar INEC, Festus Okoye ya tabbatar da dakatar da aikin tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Obingwa.

Bayanai daga Inec sun nuna cewa wasu batagari sun kutsa ofishin hukumar tare da yi wa ma'aikatan zabe barazana.

Okoye ya ce Inec za ta sake yin nazari kan lamarin kafin a dauki matsaya game da zaben jihar.

A cewar kakakin Inec, an tura kayan aikin da aka yi amfani da su a karamar hukumar ta Obingwa har da na'urar BVAS zuwa Abuja domin yin nazari a kai.

Matakin da Inec ta dauka dai bai yi wa jam'iyyu dadi ba inda tuni wasu magoya bayan jam'iyyar Labour suka fara gudanar da zanga-zanga tare da neman Inec ta gaggauta ayyana dan takararsu a matsayin wanda ya yi nasara.

Kebbi

Hukumar zabe ta Inec ta ce zabe a jihar Kebbi bai kammala ba saboda dalilai na kura-kurai da aka samu a kananan hukumomi 18 cikin 21 da ke jihar.

Ita ce jiha ta farko da aka fara ayyana zaben na ranar 18 ga watan Maris da aka fafata tsakanin manyan jam'iyyun APC da PDP a matsayin wanda bai kammala ba.

Babban jami'in tattarawa da sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Farfesa Yusuf Sa'idu ne ya bayyana matsayar Inec ranar Litinin a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Sakamakon zaben da aka sanar ya nuna cewa jam'iyyar APC na da kuri'u 388,258 yayin da PDP kuma take da kuri'un da suka kai 342,980.

Jami'in sanar da zaben ya bayyana cewa dokar zabe ta bashi ikon ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Enugu

Hukumar zabe mai zaman kanta da ke Enugu kuwa dakatar da aikin tattara sakamakon zabe ta yi a kananan hukumomi biyu na jihar saboda zargin an tafka kura-kurai.

Kakakin hukumar Festus Okoye ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin inda ya ce kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Nsukka da Nkanu East.

Ya ce an dakatar da tattara sakamakon kananan hukumomin saboda bayanai daga jami'in tattara sakamakon zaben ya nemi a soke sakamakon yankunan biyu saboda rashin yin amfani da na'urar BVAS wajen tantance masu zabe.

An dai fafata zaben gwamna na jihar ta Enugu tsakanin yan takara 17 da ke neman maye gurbin Ifeanyi Ugwanyi wanda wa'adin mulkinsa na tsawon shekara takwas ke zuwa karshe ranar 29 ga watan Mayu.