Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda gobara ta halaka tagwaye da ƴan uku a cocin Masar
Wata gobara da ta tashi ranar Lahadi a Cocin Kifdawa da ke Masar ta halaka mutum 41 cikinsu har da yara kimanin 15.
Cocin na Abu Sefein da ke gundumar Imbaba wani yanki na ma'aikata ya cika maƙil da mutane suna ibada a safiyar, da yara ƙanana da iyayensu.
Yara da dama kuma suna azuzuwa a wata makarantar rainon yara da ke hawa na farko na ginin mai hawa huɗu inda masu bincike suka ce wutar ta fara ci ne sakamakon tartsatsin wutar lantarki.
Ma'aikatar Lafiya ta ce mutane da dama sun mutu ne sakamakon shaƙar hayaƙi da suka yi da turmutsutsin da aka yi lokacin da mutane suke gaggawar neman tsira daga cocin.
A cewar ƴan uwan waɗanda suka mutu da jami'an cocin da wani asibiti da ke yankin da kafofin yaɗa labarai na Masar, cikin yaran da suka mutu har da wasu ƴan uku Mohreal da Youssef da Philopator Bassem Amir masu shekara biyar.
Yaran sun mutu ne tare da mahaifiyarsu Irina Ramzi, mai shekara 34, da kakarsu Magda Habib Nabih mai shekara 61 da kuma gwaggonsu, Mirna Atef Ramzi mai shekara 25.
Mawakiya Miretya Emad, ƴar uwa ga Magda da Irina ta wallafa saƙon jimamin mutuwarsu a shafinta na Facebook.
Ta ce "Tare da Yesu, wanda ya fi mana. Ka tuna mu a lokacin tsira".
Ba iyalin Miretya Emad ne kaɗai suka rasa yara uku ba a iftila'in. Ƴan biyu mata Mariam da Barsina Tamir Wajih masu shekara biyar da ɗan uwansu ɗan shekara uku Ibrahim na daga cikin jerin mutanen da babban asibitin Imbaba ya ambata sun mutu.
Hotunan da aka ɗauka a wajen zaman addu'oi ranar Lahadi da dare sun nuna mahaifiyarsu jikin akwatin gawarsu tana jimami tare da ɗaga ƴan yatsanta uku don alamta ƴaƴanta.
Cikin waɗanda aka ambata sun mutu har da Karolos Aryan mai shekara 10 da Mina Azmi ƴar shekara 13 da Mina Fakhir mai shekara 16.
Shafin yaɗa labarai na Copts United ya rawaito cewa ita ma mahaifiyar Karolos ta mutu. Amma ɗan uwansa Rami ya samu tsira.
Daga kan gadon da yake kwance a asibiti, Rami ya yi magana da ƴan jarida game da halin da ya shiga.
Ya ce su ukun sun halarci wani taron addu'oi tare amma suka rabu sakamakon gobarar da ta tashi sannan bai san abin da ya faru da su ba.
An ba da rahoton cewa Rami ya samu labarin halin da suke ciki ta dalilin hirar.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun rawaito wata mata wadda ta ce ta rasa yaranta biyu a gobarar, ɗaya daga cikinsu mai suna Mina.
Ta ce "Ni ce sanadiyyar rasuwarsu".
Esnad ta bayyana cewa ita ce ta tashe su domin su halarci taron addu'oin. "Mina ya faɗa min na je ranar Laraba," kamar yadda ta bayyana.
"Amma na ƙi na kuma faɗa masa cewa yau za mu je."
Limamin cocin, Abdul Masih Bakhit, mai shekara 50 na daga cikin manyan da haɗarin ya rutsa da su kamar yadda asibitin ya sanar.
An ɗauki hoton matarsa a cocin ta damƙo abin da ya yi kama da yankin kayansa da suka ƙone.