‘Majalisar dokoki ba ta bin diddigin yadda ake aiwatar da kasafin kudi a shekarun da suka gabata’

An wallafa

Masana a Najeriya sun fara tsokaci kan gazawar majalisar dokokin kasar wajen bin diddigin yadda ake aiwatar da kasafin kudi a shekarun da suka gabata.

Masanan sun yi korafin ne a daidai lokacin da majalisar dokokin kasar ke shirin fara nazari a kan kasafin kudin shekarar 2023 da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar mata.

Dr Ibrahim Shehu, malami a sashen koyon aikin gwamnati na jam'iar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma mai bincike kan yadda ake aiwatar da kasafin kudin na Najeriya, ya shaida wa BBC cewa sun samu bayanai a kan in da majalisar ta gaza, wato babban zauren majalisar ba ya zama yana duba irin korafe-korafen da ake na gazawa wajen aiwatar da kasafin kudin.

Ya ce da babban zauren majalisar na nazari a kan rahotannin da kwamitin da ke bibiyar yadda aka kashe kudaden gwamnati ya tattara da ba a fuskanci wadansu matsalolin ba.

Dr Ibrahim Shehu ya ce kwata-kwata ba a yin abin da ya kamata a majalisar.

To amma ya ce,” Ba mamaki akwai wadansu shafaffu da mai kama daga abokai ko ‘yan uwa da idan har aka bibiyi yadda ma’aikatansu ko hukumominsu suka kashe kasafin kudinsu a shekara to lallai za a iya binciko wata badaka a ciki.”

Malamin jami’ar ya ce bayanan da suka samu daga majiya mai tushe sun nuna cewa akwai rahotannin kwamitin da ke bibiyar yadda aka kashe kudaden gwamnati a ajiye tun daga shekarar 1999 kawo 2022 majalisa ba ta taba duba suba ballantana su dauki matakan da ya dace.

Ya ce ” Da majalisar tana duba irin wadan nan rahotanni, to ko shakka ba bu da shugabanni  hukumomi da ma’aikatun gwamnati za su shiga taitayinsu.

Dr Ibrahim Shehu, ya ce idan da sun san cewa majalisa za ta duba wadan nan rahotanni har a dauki mataki a kansu, to ba bu shakka duk wata badakala ta cin hanci ko satar kudin al’umma za ta ragu ko kuma ma a kawar da ita baki Daya.

A makon da ya gabata ne dai shugaban Najeriya ya gabatar wa zauren majalisar kasafin kudi, wanda ya kunshi kudi sama da naira tiriliyan ashirin, kuma shi ne kasafin kudi na karshe da shugaban zai gabatar kafin saukarsa mulki a shekara mai zuwa.