Yarinyar da aka kulle a gida har shekara bakwai a Jamus

An wallafa

Ana binciken mahaifiyar wata yarinya 'yar shekara takwas da kakaninta bayan masu gabatar da kara a Jamus sun ce an kulle ta tsawon shekara bakwai.

 

Daga bisani an  sako ta daga gidan a ƙarshen watan Satumba kuma yanzu tana karkashin kulawar mahukunta.

Jami'an kula  da jin dadin jama'a sun ce  yarinyar tana fuskantar matsaloli wajen gudanar da ayyukan yau da kullum kamar hawan matakala.

Kafofin yada labaran Jamus sun ce ba ta taba ganin daji ko wurin kiwo ba.

Gidan da ke Attendorn a yankin Sauerland na yammacin Jamus ba wani wuri ne mai kyau ba.

Sai dai masu gabatar da kara sun ce a cikin wannan gidan ne mahaifiyar yarinyar da iyayenta suka nesanta ta daga duniya har tsawon shekara bakwai.

Sun ce babu wata shaida da ta nuna cewa an gallaza mata ko tana fama da ciwon tamowa.

Shugaban hukumar kula da jin dadin yara na yankin, Micheal Farber ya ce yarinyar ta iya karatu da lissafi amma tana fuskantar matsaloli wajen gudanar da ayyukan yau da kullum. ’’Za mu ga yadda hakan zai kasance," in ji shi.

A yanzu tana karkashin kulawar masana ilimin halayyar yara.

Wani kwararre daga kungiyar kare hakkin yara ta kasa ya shaida wa kafofin yada labaran Jamus cewa: "Duniya a halin yanzu ta juye ga mata. Za ta ji kamar tana wata duniya daban."

A yanzu masu gabatar da kara na kokarin  gano musababbin abin da ya faru.

Sun ce mahaifiyar yarinyar da kakanninta sun yi shuru a kan alamarin kuma kawo yanzu ba su samu wata shaida ba.

Sai dai ana kyautata zaton cewa uwar ta yi kokarin hana yarta haduwa  da mahaifinta ne, wanda ta rabu da shi jim kadan kafin a haifi yarinyar.

Rahotanni sun ce ta hana shi mu'ammala da yarinyar abin da ya sa ya garzaya kotu inda aka bai wa dukaninsu izinin kula da ita a shekarar 2016.

A wancan lokaci mahukuntan kasar da mahaifin yarinyar sun yi amannar cewa mahaifiyar ta bar kasar da yar tata.

A shekarar 2015 ta sanar da su a hukumance cewa ta yi kaura zuwa Italiya.

A yanzu masu gabatar da kara sun yi amanar cewa a zahiri ba ta taba barin kasar ba kuma suna zaune ne tare da kakannin yarinyar wadanda ake ganin sun taimaka mata ta ci gaba da rayuwa irin wannan.

Sai dai mutane da dama sun nuna mamaki a kan yadda yarinyar ta kasance a boye na dogon lokaci ba tare da wani ya yi ido biyu da ita ba a karamin gari mai mutane dubu 24.

An bayyana cewa an samu wasu da suka tsegunta wa mahukunta a kan yarinyar a shekarun baya-bayan nan, sai dai sun ce lokacin da suka gudanar da bincike ba su samu kwakkwarar shaidar da ta nuna cewa ana rike da yarinyar a cikin gidan ba.

 A watan Yunin bana  wasu ma'aurata sun bayar da rahoton cewa sun yi tozali da yarinyar  abin da ya sa aka gudanar da bincike da ya gano cewa ita da mahaifiyarta ba su taba  zama a Italiya ba kuma wannan shi ne sanadin gano ta a gidan kakannin nata.