Shugabar masu ra'ayin ra'ayin rikau da take dab da cin zabe a Italiya

Giorgia Meloni,  ta tsaya daukar hoto bayan kammala tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, a birnin Roma na kasar Italiya 24 ga a watan Agusta Rome, Italy, August 24

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Giorgia Meloni, mai shekara 45, ita ce shugabar jam'iyyar masu ra'ayin rikau
An wallafa

Sama da shekaru 40 kenan da Anna Maria Tortora ke sayar da nunannun tumatur da kukomba ga abokan huldarta a wata kasuwa da ke birnin Roma.

Ba ta taba kawowa ran ta wata 'yar yarinya da ke bin layin sayen kayan rike da hannun kakanta wata rana za ta zama firaiministar kasar ba.

"Mutumin kirki ne", in ji ta, "ya kuma matukar kaunar jikarsa."

Yayin da 'yar karamar yarinyar da ta rikide, shugabar jam'iyya, har kuma Giorgia Meloni, ta kawo wannan mataki kuma a karon farko, Anna Maria ta na cike da alfahari.

"Na taimakawa girmanta sosai! waken da suke siya nan ya inganta girmanta, domin ta na ci ta koshi sosai."

Kasuwar da ke Garbatella, yankin ma'aikata ne da ke birnin Roma, masu bin tafarkin gargajiya sosai.

Lamari ne mai ban mamaki a siyasa, da za a samu mace ta farko mai ra'ayin rikau da zama firaiminista tun bayan wadda ta gabata Benito Mussolini.

Zaben Italiya da aka gudanar gabannin lokacinsa ya sanya shugaba Sergio Matteralla zai bukaci shugabannin jam'iyya su zabi wanda zai jagoranci gwamnati.

Sai dai Mis Meloni da ke sahun gaba, ka iya ƙin amincewa.

"Gaskiya ba ta walkiltar wannan zamanin," in ji Marta, wata mai sayan kayan masarufi dda ke tura dan keken dakon kaya a kasuwar kayan lambu.

Dattijuwar mahaifiyarta, Luciana ta shaida min a tsorace ta ke. "Ni karan kaina ba na bin irin ra;'ayinta na riƙau," in ji ta.

"Idan har ta yi nasara, za mu shiga lokaci maras kyau."

 Anna Maria mai saida kayan lambu
Bayanan hoto, Anna Maria mai saida kayan lambu, da Giorgia Meloni ke ci tun tana karama har girmanta
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A bayyane ta ke ƙarara Meloni na adawa da mulkin danniya, a bidiyo na baya-bayan nan da ta yi da harshen Ingilishi, da Sifaniya da Faransa ta nanata ba ta goyon bayan tsohuwar al'ada.

Sai dai tarihi shi ne babban matsalar kasar kamar dai Jamus bayan yaki, sun bar masu mulkin danniya yin sauye-sauye a tsarin mulki.

A shekarar 2012 ne aka samar da jam'iyyar Brothers of Italy, ta samo na ta asali daga jam'iyyar Social Movenent, da aka samar daga jam'iyyar da Mussolini ta samar.

Jam'iyyar ta ci gaba da amfani da tambarinta d aka yi amfani da shi gabanni da bayan yaki, wato tambari mai dauke da tashin wuta a tsakiya, ana yi wa hakan kallon cin wuta a kabarin Mussolini.

"Giorgia Meloni ba ta son sauyata, saboda shi ne abin da ba za ta iya kaucewa ba a matsayin siyasarta, kuruciyarta na da alaka da wannan," in ji Gianluca Passarelli, farfesakan kimiyyar siyasa a jami'ar Sapienza ta Roma.

"Jam'iyyarta ba ta danniya," ya yi karin bayani. "Danniya na nufin wadanda suka samu mulki da lalata tsarin shi.

Ba za ta yi haka ba, ba ma za ta iya ba. Sai dai jam'iyyar na dauke da mutane da dama da suka shigo daga wasu jam'iyyun da takamaimai ba a san bangaren da suka rinjaya ba. Ita dai ta na tsakiya kawai."

Kuruciyarta ta kasance mai cike da kalubale, ta wani fannin kuma mabudi ga wata nasara, matashiyar d ake girmmawa da soyuwa ga mutane.

An haife ta a Roma, shekarar ta daya kacal mahaifinta, Francesco ya fice daga gida tare da komawa tsuburin Canary.

Francesco mai sassaucin ra'ayi ne, mahaifiyarta Anna mai ra'ayin rikau ce, dalilin da akai ta yada jita-jitar rashin zaman iyayenta wuri guda ya kara ta'azzara kasancewarta mai ra'ayin rikau, saboda rashin zama tare da mahaifinta.

Daga baya sun koma Garbatella, kusa da kakanninta. Tana da shekara 15 ta shiga sahun gaba a wakilcin matasa da su ke adawa da mulkin danniya MSI, daga bisani ta zama shugabar dalibai a kawancen jam'iyyar National Alliance.

Marco Marsillo ya na tattaunawa da wakilan MSI a Garbatella, a lokacin da Giorgia Meloni ta kwankwasa kofa a shekarar 1992.

Ya girme ta da shekara 10, ya zama babban amininta kuma kawancen siyasa, a yanzu kuma ya zama shugaban yankin Abruzzo.

"To fa ga budurwarsa, da kodayaushe ta ke maida hankali kan abin da ta sanya gaba ," in ji shi. "Ka gane ta saboda taron da aka yi na dalibai, za ta takawa ko waye birki idan ya tunkaro ta domin karbe makirifo."

Shekaru da dama, iyalan na zuwa hutu, mahawara, da tarukan jama'a, ya kuma dade ya na nazari akan ta tun tana karama da yadda ta ke bai wa kanta kwarin gwiwa.

"A wancan lokacin ta na da abubuwan da ba su kwanta a ran ta ba," in ji Mr Marsilio, "amma watakil wannan ne kwarin gwiwar da ta samu, da ya sanya ta zama jajirtacciya, ba raguwa ba musamman ta fuskar magance matsalolin da ke tasowawa."

A shekarar 2008, lokacin ta na 'yar shekara 31, Giorgia Meloni ta zama matashiyar ministar Matasa da Wasanni a Italiya, kuma shugaba Silvio Berlusconi ne ya nada ta.

Bayan samar da jam'iyyarta a shekarar 2012, ta yi nasara da kashi 40 na kuri'un da aka kada a shekarar 2018.

Giorgia Meloni, shugaban jam’iyyar  Brothers of Italy, Silvio Berlusconi, shugaban jam’iyyar masu sassauci ta Forza Italia, shugaban kungiyar arewacin Italiya Matteo Salvini, sun dauki hoto lokacin ziyarar aiki a Tempio di Adriano a Roma ranar 1 ga watan Maris 2018
Bayanan hoto, Giorgia Meloni na fatan kafa gwamnatin masu ra'ayin rikau, anan ta na tare da Silvio Berlusconi (tsakiya) da Matteo Salvini

Ko a yanzu da ta ke kokarin tabbatarwa aminan Italiya na kasashen yamma babu abin da zai sauyata, akwai abin da ake nuna damuwa akai, misali bai wa Ukraine cikakken goyon baya kamar yadda gwamnatin Dragi ke yi, ana nuna damuwa kan batutuwa masu sarkakiya da take adawa da su karara babu boyo.

''Eh akwai batun iyalai, da auren jinsi'', kowa ya bata amince da su ba, ta kuma yi bayani a gangamin yakin neman zabe a Sifaniya.

Ta yi kiran a dauki mataki mai tsauri kan 'yan ciranin da ke shiga turai daga Libya.

"Babu wani hadari da ke tattare da Meloni, ta fuskar dimukradiyya, amma fa hatsari ce ga kungiyar Tarayyar Turai," in ji farfesa Passarelli, wanda ya sanya ta a sahun 'yan siyasar kasashen Hungary da Faransa.

"Tafiyarsu daya da Marine Le Pen ko Viktor Orban. Kuma ta na son sanya Turai gaba.

Italiya ka iya zama wata mai sassauci ga Putin domin, ya ci gaba da karya lagon Turai.''

Ga aminanta, ta na wakiltar gangamin sauya tsarin siyasar Italiya da kasar ke tsananin bukata a yanzu, da bai wa tattalin arzikin kasar takin da zai kara bunkasa.

"Ina jin dadi, tamkar Uban da ya kama hannun 'yarsa, ya shiga da ita dandalin da za a daura mata aure," in ji Marco Marsilio.

"Inda ba mu da kwarin gwiwar za ta yi abin da ya dace, ai ba za mu saki jiki da samar da jam'iyyar ba."

Amma me ya ke shirin fada ma ta da zarar jam'iyyarsu ta yi nasara?

"Je ki gaba gadi, za ki iya!", amsar da ya bada kenan.

"Mun dade mu na fatan haka. Mun dade mu na jiran lokacin."