Yadda ake tsangwamar masu cutar da ke jirkita halitta a Najeriya
Yadda ake tsangwamar masu cutar da ke jirkita halitta a Najeriya
An wallafa
Dysplasia wata cuta ce da ke shafar ƙwayoyin halittar mutum har ta jirkita su.
Ƙwararru sun ce cutar ba ta da alaƙa da kansa amma ta kan sauya yanayin kamannin waɗanda ta shafa.
Masu fama da wannan cuta suna da yawa a Najeriya, kuma suna kokawa kan irin wariya da tsangwama da suke fuskanta daga al'umma.
Hakan na faruwa ne saboda ƙarancin wayar da kan mutane. Sai dai akwai wata cibiya da ke aiki don taimakon masu cutar da kuma ƙoƙarin wayar wa da mtane kai a kanta.
A wannan bidiyon, BBC Hausa ta tattauna da mai fama da irin wannan cuta da ke zaune a Abuja, babban birnin ƙasar.



