Sadio Mane ya koma yin atisaye da Bayern Munich bayan jinya

An wallafa

Sadio Mane ya koma karbar atisaye a Bayern Munich ranar Talata, bayan raunin da ya yi jinya.

Daf da za a fara gasar cin kofin duniya a cikin Nuwambar 2022 a Qatar, Mane ya ji ciwon da ya hana shi wakiltar Senegal a babbar gasar tamaula ta duniya.

A wani faifan bidiyo da Bayern ta saka a shafinta na Twitter an ga tsohon dan wasan Liverpool na atisaye a cikin filin Munich da kankara ta lullube.

Mane, mai shekara 30 ya ji rauni a kafarsa ta hagu a wasan da Bayern ta caskara Werder Bremen 6-1 ranar 8 ga watan Nuwambar 2022.

Daga nan ne aka yi masa tiyata, wanda ya yi jinyar da ta hana shi buga gasar kofin duniya da aka yi a Qatar, wanda Argentina ta lashe na uku jumulla

Kociyan Bayern, Julian Nagelsman ya fada a cikin Janairu cewa yana sa ran Mane zai buga wa Bayern Champions League da Paris St German ranar 8 ga watan Maris.

Sai dai kuma Mane ba za yi wa Bayern wasan da za ta karbi bakuncin Cologne ba ranar Talata, domin bai kammala komawa kan ganiya ba.