Abin da ya kamata ku sani kan wasan Brazil da Koriya ta Kudu

Brazil

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Tawagar Brazil za ta kara da ta Koriya ta Kudu a wasan zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.

Brazil mai kofin duniya biyar za ta fafata da Koriya a filin wasa da ake kira 974 ranar Litinin.

Brazil ta kawo wannan matakin, bayan da ta ja ragamar rukuni na bakwai da maki shida, ita kuwa Koriya ta Kudu ita ce ta biyu a rakuni na takwas da maki hudu.

Wannan shi ne karo na takwas da za su fafata a tsakaninsu, amma a wasan farko a babbar Gasar Tamaula ta duniya - Brazil ta ci shida da rashin nasara daya.

A cikin watan Yuni tawagogin biyu sun hadu a wasan sada zumunta, inda Brazil ta yi nasara da ci 5-1.

Wasa hudu daga 10 a baya Brazil ta yi rashin nasara a Gasar Cin Kofin Duniya.

Wannan shi ne karon farko da Koriya ta Kudu za ta buga wasan zagaye na biyu a babbar Gasar Kofin Duniya tun bayan 2010.

A shekarar Uruguay ta doke Koriya a zagayen kungiyoyi 16 a wasannin.

Brazil ta haura karawar zagaye na biyu a wasa bakwai baya a babbar Gasar tamaula ta duniya.

Rabonda a fitar da Brazil a wannan zagayen na tawagogi 16 tun 1990, bayan da Argentina ta doke ta a Gasar.

Wasa da aka kara tsakanin Brazil da Koriya ta Kudu

2022/2023

Wasan sada zumunta Alhamis 2 ga watan Yuni    

  • South Korea     1 - 5 Brazil       

2018/2019

Wasan sada zumunta Talata 19 ga watan Nuwambar 2019        

  • Brazil       3 - 0 South Korea    

2013/2014

Wasan sada zumunta Asabar 12 ga watan Oktoban 2013     

  • South Korea     0 - 2 Brazil       

2002/2003

Wasan sada zumunta Laraba 20 ga watan Nuwambar 2002       

  • South Korea     2 - 3 Brazil       

1998/1999

Wasan sada zumunta Lahadi 28 ga watan Maris 1999           

  • South Korea     1 - 0 Brazil       

1997/1998

Wasan sada zumunta Lahadi 10 ga watan Agusta 1997           

  • South Korea     1 - 2 Brazil       

1995/1996

Wasan sada zumunta Asabar 12 ga watan Agusta 1995          

  • South Korea     0 - 1 Brazil