Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda mahaifiyar Deborah ta ji da kisan 'yarta kan zargin ɓatanci ga Annabi
Wasu mutane da aka kashe 'yan uwansu sakamakon zargin sun yi ɓatanci ga addinin Musulunci sun bayyana wa BBC irin halin da suke ciki bayan kisan nasu.
Alheri Emmanuel, mahaifiyar matashiya Deborah Samuel - matashiyar da aka kashe a Jihar Sokoto - ta ce ta ji kamar an soka mata mashi lokacin da ta samu labarin kisan 'yar tata.
Ita ma Zainab Ahmed, matar wani ɗan banga da aka kashe a Abuja bisa zargin ɓatanci ga Annabi Muhammadu S.A.W. ta ce ba za ta yafe wa waɗanda suka kashe mijin nata ba.
Cikin wannan bidiyo na musamman, duk da malaman addinin Musulunci sun jaddada cewa "duk wanda aka tabbatar ya yi ɓatanci ga Annabi hukuncinsa kisa ne", amma sun ce ba mutanen gari ne za su zartar da hukuncin ba.