Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sukar da ake yi wa Fernandes hassada ce - Ten Hag
Kocin Manchester United Erik Ten Hag ya zargi Nottingham Forest da kai wa Bruno Fernandes mummunar suka a wasansu na zagaye na biyar a gasar FA Cup , ya kuma kira masu sukar kyaftin dinsa a matsayin mahassada.
Fernandes ne ya kawo ƙwallon da Casemiro ya ya ci a minti na 89 wanda ta bai wa United ketarawa zuwa zagayen quater-final inda za ta fafata da Liverpool.
Ɗan wasan na Portugal ya sha suka a shafukan sada zumunta, bayan da Fulham ta doke United a gida ranar Asabar, inda ya yi rashe-rashe a ƙasa bayan karo da suka yi da Sasa Lukic sannan ya zabura don bayar da gudumawa wurin kai hari.
"Kun ga cewa ƴan wasan Forrest na ta kai masa hari," in ji Ten Hag. "Duk lokacin da ya samu ƙwallo sai a afka masa''.
Amma a nasa ɓangaren kocin Nottingham Forrest, Nuno Espirito Santo ya musanta cewa ƴan wasansa sun mastawa Fernandes.
"Ba na tunanin haka," in ji Nuno, lokacin da aka tambaye shi ko ƴan wasansa sun takura Fernandes. "Ban ga abin da Erik ya gani ba.''