Barca za ta yi binceken cin zarafin da aka yi wa Vinicius

An wallafa

Barcelona za ta yi ''bincike' kan cin zarafi'' bayan rahoton cewar an ci zarafi ɗan ƙwallon Real Madrid ranar Asabar a karawar El Clasico.

Real Madrid ce ta yi nasara a wasan na mako na 11 a La Lida da cin 2-1, inda Jude Bellingham ya ci wa Real ƙwallayen a karawar da suka yi a Lluis Companys Olympic Stadium.

Inda ake zargin an ci zarafin dan wasan mai shekara 23, a lokacin da za a sauya shi a karawar daf da tashi fafatawar.

Ita ma hukumar gudanar da gasar La Liga ta Sifaniya ta ce za ta yi bincikenta.

A wani jawabi da ta fitar a kafar sada zumunta hukumar ta ce ''tana aiki tare da wasu da za su nuna mata waɗanda suke da hannu a cin zarafi, sannan a miƙa su wajen hukuma.''

Ita kuwa Barcelona cewa ta yi ''Za mu ci gaba da tsare martaba da kimar ɗan ƙwallon da wasan da mutunta wadanda muke taka leda, za mu yi bincike don zaƙulo ko an ci zarafi a ranar Asabar.''

Vinicius, wanda aka ci zarafi a irin wasan nan na hamayya a bara, ya yaba wa Sevilla a makon jiya, wadda ke sukar cin zarafin ɗan kwallo da kai rahoto ga mahukunta.

Wani hoto da ɗan wasan tawagar Brazil ya saka a kafarsa ta sada zumunta ya nuna wani mutun na cin zarafinsa.

Tun farkon watan nan ya bayar da shaida kan wasu mutum uku magoya bayan Valencia da ake tuhuma da cin zarafin ɗan ƙwallo a watan Mayu a Estadio Mestalla.