'Yadda cutar laka ta hana ni cimma burina na zama likita'

'Yadda cutar laka ta hana ni cimma burina na zama likita'
An wallafa

Khadijah Abba, mai shekara 22, ta samu matsalar laka sakamakon wani hadarin mota da ta yi tsakanin Zaria da Kano shekaru 22 da suka gabata.

Khadijah ta kasance a cikin tawagar masu buga wa jihar Borno kwallon hannu kuma hadarin ya same ta a kan hanyarsu ta tafiya Italiya.

"Lokacin da muka yi wannan hadari ne na samu wannan larura amma kuma babu abin da gwamnatin jihar Borno ta lokacin ta yi min.

Hakan ne ya sa na ma bar garina na Maiduguri na koma birnin Gombe inda nake sana'ar dinki hula sannan kuma jama'a na taimaka min.

Na shiga kungiyar masu nakasa tunda dai na riga na samu nakasa." Yanzu haka dai Khadijah ba ta iya fitsari sai da robar yin fitsari. "Burina shi ne na samu na zama likita idan har na samu aka yi min aiki na samu lafiya."

Yayin da a yau ake tuna wa da masu irin larura, Khadijah na kira ga al'umma da su rungumi masu wannan ciwo kasancewar zai iya samun kowa.