Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Al-Ittihad ta yi shiri kan Salah, Chelsea ta kamma batun dauko Ceicedo
Saudiyya ta ce kungiyar Al-Ittihad za ta yi wa Liverpool tayin kusan fam miliyan 60 kan dan wasa Mohamed Salah, sun kuma shirya tsaf domin bai wa dan wasan gaban na Masar fam miliyan 155 kan kwantiragin shekara biyu. (Al Riyadiah - in Arabic)
Saudiyyar dai na kokarin dauko zakakuran ‘yan wasan da ake ji da su a Premier League, ciki har da dan wasan Manchester City da Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 32, a shekara mai zuwa (Mirror)
Barcelona ta shiga yarjejeniyar hadin gwiwa kan dan wasan Portugal da ke taka leda a Manchester City wato Joao Cancelo, mai shekara 29, da Bernardo Silva, mai shekara 28 – kuma a shirye suke don tabbatar da hakan a kaka mai zuwa. (Sport - in Spanish)
Kokarin da Arsenal ke yi kan mai tsaron ragar Sifaniya da ke taka leda a Brentford David Raya, mai shekara 27, na gab da kammaluwa, daidai lokacin da dan wasan Gunners kuma na bayan Amirka Matt Turner, mai shekara 29, ya hirya domin komawa taka leda a Nottingham Forest. (Fabrizio Romano)
Sai dai Nottingham Forest na tattaunawa kan daukar tsohon mai tsaron ragar Leicester City Kasper Schmeichel, mai shekaru 36, daga Nice. (Eurosport Denmark)
Shi kuwa dan wasan Paris St-Germain, na gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 24, zai yi kakar wasa a Premier League a matsayin aro, kafin ya koma kungiyar Real Madrid da ya jima ya na mafarkin taka ma ta leda. (Mirror)
Chelsea ta shirya kara kudin daukar dan wasan tsakiya na Brighton Moises Caicedo bayan matashin dan wasan Ecuador mai shekara 21-ya fice daga wasan sada zumunta da Rayo Vallecano. (Telegraph - subscription required)
Dan wasan Fulham Tosin Adarabioyo, mai shekara 25, ya kaucewa batun komawa kungiyar Tottenham, saboda mai kai hari na Ingilar na son komawa Monaco. (Sun)
Crystal Palace na tattaunawa kan yarjejeniyar aro dan wasan , Bayer Leverkusen kuma na mai tsaron gid ana Ivory Coast Odilon Odilon Kossounou, 22, ya yin da Eagles fakon dan wasan Chelsea da Ingila ajin shekara -21 wato Lewis Hall, mai shekara 18. (Mail)