Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed Salah: Ina nan daram a Liverpool
Dan kwallon Liverpool, Mohammed Salah ya ce "tabbas" zai ci gaba da kasancewa a kungiyar a kakar wasa mai zuwa amma kuma ya ki bayyana ko zai sabunta yarjejeniyarsa ko kuma a'a.
Yarjejeniyar Salah da Liverpool za ta kare ne a watan Yunin 2023 abin da ya janyo ake jita-jitar zai bar Anfield.
"Tabbas zan kasance a nan a kakar wasa mai zuwa. Abin da ke gabanmu shi ne lashe gasar Champions".
Takwaransa dan kasar Senegel, Sadio Mane, ya ce zai bayyana matsayinsa kan ganiyar bayan sun taka leda da Real Madrid a birnin Paris.
Dan kwallon Senegal din ya zura kwallo 120 a cikin wasa 268 da ya buga wa Liverpool kuma kungilarsa da kungiyar za ta kare ne a watan Yunin badi.