Mahaifin Ansu Fati na jin haushin Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Mahaifin Ansu Fati, Bori Fati ya ce baya jin dadin yadda Barcelona ke ajiye yaron yana dumama benci.
Ya ce zai so yaron mai shekara 20 ya koma wata kungiyar da taka leda, amma a zabinsa gwara ya zauna a Camp Nou, wadda ya fara tun yana karami.
''Ina jin haushin rashin saka shi a wasa yadda ya kamata, sai dai ya buga minti daya ko biyu ko uku, hakan yana bakanta min rai,'' in ji Bori kamar yadda ya sanar da wani gidan rediyo a Sifaniya.
''Ni ba zan ce sai a saka shi a wasa ba ko ta halin kaka, saboda dukkan 'yan wasan Barca da ke ci mata kwallaye suna da kayu, kuma suna gabansa, amma ina magana ne kan Ansu Fati,'' kamar yadda ya sanar da Cadena Cope.
''Muna magana ne kan dan kwallon tawagar Sifaniya mai saka riga mai lamba 10 a Barcelona, yaron da ya fara kungiyar daga La Masia.''
Ansu Fati ya fara yi wa Barcelona tamaula a 2019 yana da shekara 16 da haihuwa a lokacin, wanda ya nuna kansa a fannin tamaula.
To sai dai dan wasan ya ji rauni a gwiwar kafarsa a 2020, hakan ya sa ya yi jinya mai tsawo da yawa.
A shekarar 2021 ya karbi riga mai lamba 10 da Messi ya ajiye, wanda ya koma Paris St Germain da taka leda.
Ansu Fati baya buga sosai karkadhin Xavi, wanda ya yi karawa tara, duk da cewar yana da koshin lafiya.
A baya Bori Fati ya tattauna da wakilin dan sa, Jorge Mendes, kan batun makomar yaron a Barcelona.
''Lokacin da na gana da Jorge ya sanar da ni cewar Ansu Fati, baya son barin Barcelona, yana son ci gaba da zama a kungiyar duk wuya duk dadi.
''A matsayin mahaifinsa ina wani tunanin na da ban, saboda na san abubuwan da suke gudana.''
An tambaye shi ko zai yadda Ansu Fati ya bar Barcelona idan abubuwa ba su sauya ba, sai Bori Fati ya ce ''Kwarai kuwa.''
Ya kara da cewar ba ya zuwa kallon wasannin Barcelona, saboda ransa yana baci kan abin da Barcelona ke yi wa dansa.











