Mun shirya kawar da almajirai daga kan titunan Najeriya - Sharada

Mun shirya kawar da almajirai daga kan titunan Najeriya - Sharada
An wallafa

Shugaban hukumar kula da ilimin almajirai ta Najeriya, Sha'aban Ibrahim Sharada ya hukumarsa ta ƙuduri aniyar kawar da aƙalla yara miliyan 10 da ke gararamba a kan titunan kasar, domin mayar da su makaranta.

Sha'aban Sharada ya ce a ƙididdigar da UNESCO ta fitar ya nuna cewa akwai kimanin yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, don haka ne hukumarsa ta ƙuduri aniyar magance wannan matsala.

Ya ƙara da cewa hukumarsa ta aƙuduri aniyar zamanatar da karatun almajirci ta yadda almajirai za su samu ilimin boko, kamar lissafi da karatun boko.

Ya ce a kowace shekarar hukumar za ta samar da santoci ta hanyar yi wa makarantun tsangaya rajista don cin moriyar sabon tsarin.

''Hukumarmu za ta riƙa bai wa almajirai takardun shaidar halartar kammala karatu''.

Sha'aban Sharada ya kuma ce hukumar za ta ƙirƙiri makarantu na dare ko na ƙarƙashin bishiya domin bayar da dama mutanen da suka girma ba su yi ilimi ba, domin su samu ilimi.

Ya ce za a inganta harkokin makarantun tsangaya domin samun damar ilimantar da almajirai ilimin zamani.