Arsenal ta ci gaba da jan ragamar zaren Premier League

An wallafa

Arsenal ta caskara Bournemouth 3-0 a wasan mako na 36 a Premier League ranar Asabar a Emirates.

Gunners ce ta mamaye mintin 45 din farko, sannan ta fara cin kwallo a bugun fenariti tun kan hutun rabin lokaci.

Golan Bournemouth, Mark Travers ne ya yi wa Kai Havertz keta, inda Bukayo Saka ya yi bugun daga kai sai mai tsaron raga ya kuma ci kwallon.

Arsenal ta kara na biyu a minti na 70 ta hannun Leandro Trossard daga baya Declan Rice ya kara na ukun da ya bai wa Gunners maki ukun da take bukata.

Daga baya Bournemouth ta saka matsi ko za ta zare kwallaye, har ma Dominic Solanke ya nemi cin kwallo, amma David Raya ya tare, bayan da suka koma zagaye na biyu.

Antoine Semenyo ya ci Arsenal kwallo, amma aka soke da cewar tun kan nan Solanke ya yi wa David Raya keta.

Haka shima mai tsaron bayan Arsenal, Gabriel ya ci kwallo, amma rafli ya ce an yi satar gida.

Wasa na takwas kenan da Bournemouth ta kasa cin Arsenal, wadda ta ci bakwai daga haduwa baya.

Wasa daya ne Bournemouth ta yi nasara a kan Arsenal daga 16 da suka yi a baya, shi ne a cikin Janairun 2018.

Da wannan nasarar Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a teburin Premier League da tazarar maki hudu tsakaninta da ta biyu Manchester City.

Idan anjima ne City za ta kara da Wolverhampton ranar Asabar a dai babbar gasar tamaula ta Ingila.

A karawar an dan yi shiru na minti daya, domin girmama mai goyon bayan Arsenal, Daniel Anjorin dan shekara 14, wanda aka kashe da takobi ranar Talata.

Arsenal za ta je je gidan Manchester United a wasan mako na 37 a gasar ta Premier League.