Barcelona za ta fadada Camp Nou a 2023/24

An wallafa

Barcelona ta tabbatar da cewar za ta buga wasannin kakar 2023/24 a filin wasa na Olymic, bayan da za ta fara gyaran Camp Nou.

Sai dai kungiyar za ta buga kakar da za a fara a cikin watan Agusta a filin Camp Nou, daga nan ta koma filin Olympic da zarar an kammala kakar badi.

Tsohon filin wasa na Espanyol shi ne na biyar a yawan cin 'yan kallo a Sifaniya da suka kai 60,713, wanda ya karbi bakuncin wasannin Olympic a 1992.

Barcelona na fatan Camp Nou mai cin 'yan kallo 99,000 zai koma karbar mutum 110,000 - hakan zai sa ya zama na farko mai daukar 'yan kallo da yawa a duniya.

Cikin gyare-gyaren da kungiyar za ta yi bayan fadada wajen zaman 'yan kallo, sama rifin za a samar da na'urar da za ta ke dumama filin da sanyaya Camp Nou.

Abokiyar hamayyar Barcelona, Real Madrid ta gyara filin wasa na Santiago Bernabeu a kakar 2020/21.

Ta koma buga wasanni a Estadio Alfredo Di Stefano a lokacin da 'yan kallo ba sa halartar wasanni, don gudun yada cutar korona.