Real Madrid ta fara karyawa da Almeria a La Liga ta bana

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta fara La Liga da kafar dama, bayan da ta je ta doke UD Almeria da ci 2-1 a wasan makon farko a kakar 2022/23 ranar Lahadi.
Minti shida da fara wasa Almeria ta fara cin kwallo ta hannun Largie Ramazani.
Sai da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Real ta farke ta hannun Lucas Vazquez daga baya David Alaba ya ci na biyu.
Real Madrid ce ta lashe kofin La Liga kakar da ta wuce, kuma na 35 jumulla ba wadda ta kaita daukar kofin babbar gasar tamaula ta Sifaniya a tarihi.
Kungiyar Almeria ce ta yi ta daya a gasa mai daraja ta biyu a bara da ake kira Segunda Division,, hakan ya sa kai tsaye ta samu tikitin buga La Ligar bana.
Almeria ta koma buga La Liga, bayan kaka bakwai rabonta da wasannin.
'Yan wasan da koci Carlo Ancelotti ya je da su Almeria a wasan makon farkon.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis Lopez.
Masu tsaron baya: E. Militao, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modric, Camavinga, Casemiro, Valverde, Lucas V., Tchouameni da kuma D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr. da kuma Mariano.
Real Madrid mai harin lashe kofi biyar ko shida a bana ta dauki Uefa Super Cup, bayan da ta ci Eintranch Frankfurt 2-0 ranar Laraba a Helsinki.
Real na fatan cin La Liga da Copa del Rey da Spanish Super Cup da Champions League da kuma Fifa Club World Cup a kakar nan.
A bara Real Madrid ta dauki kofi uku da ya hada da Spanish Super Cup da La Liga da kuma Champions League.









