Ɗan bindiga ya buɗe wuta kan kiristoci masu ibada a Jamus

Asalin hoton, Reuters
Wani ɗan bindiga ya kashe mutum bakwai tare da raunata wasu da dama a harin da ya kai kan taron kiristocin ɗariƙar Jehovah’s Witness a birnin Hamburg na Jamus.
Ƴan sanda sun ce mutumin ya yi gaban kansa ne a harin da ya kai ranar Alhamis, kuma an kyautata zaton shi ma ya mutu. Sun kuma ce har yanzu babu takamaiman bayani kan maƙasudin harin.
Mujallar Der Spiegel ta ruwaito cewar maharin ya kasance ɗaya daga cikin ƙungiyar addinin a baya.
Yanzu haka dai ana ci gaba da bincike a wurin da lamarin ya faru, sai ba a tantance waɗanda lamarin ya rutsa da su ba.
Ƴan sanda sun ce sun tsinci gawar wani mutum a wurin, wanda suke kyautata zaton na maharin ne.

Asalin hoton, Reuters
Mai magana da yawun ƴan sanda a gundumar Der Spiegel, Holger Vehren ya ce an kira ƴansandan da misalain ƙarfe 9:15 na dare a ranar Alhamis, inda aka ba su rahoton jin harbe-harbe a wani gini da ke kan titin Deelboge.
Ya ce “jami’an da suka je wurin sun iske mutane waɗanda suka samu munana raunuka, ‘waɗanda ake zargin na harbin bindiga ne.”
Ana tunanin cewa harin ya faru ne a lokacin da mutane suka taru domin yin muraji’ar littafin bibble.
Wakilin BBC a wurin ya ruwaito cewa masu gwajin kwayar halitta sun shafe dare su na gwaje-gwaje a wurin cikin tsananin sanyin dusar kankara.
Magajin birnin Hamburg Peter Tschentscher, ya bayyana kaɗuwa kan wannan hari.

Asalin hoton, Reuters











