Tinubu ya naɗa Badaru ministan tsaro, Wike ministan Abuja

An wallafa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa tsohon Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru ministan tsaron ƙasar.

Kazalika, tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ne zai taimaka masa a matsayin ƙaramin ministan tsaro.

Tsohon Gwamnan jihar Ribas da ke kudancin ƙasar, Nyesom Wike, shi ne ministan Abuja, yayin da Mariya Mairiga daga Kano za ta yi aiki a matsayin ƙaramar ministar Abuja.

Wata sanarwa ce daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana sunayen ministocin da ma'aikatunsu a yammacin Laraba.

Mutum 45 cikin 47 majalisar dattawa ta tantance kuma ta tabbatar a matsayin ministocin na Tinubu, abin da ke nufin za a sanar da sauran nan gaba.

Ga jerin sunayen ministocin da ma'aikatunsu:

  • Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijita - Bosun Tijani
  • Ƙaramin Ministan Muhalli - Ishak Salaco
  • Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki - Wale Edun
  • Ministar Harkokin Teku da Tattalin Arziki - Bunmi Tunji
  • Ministan Lantarki - Adedayo Adelabu
  • Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Al'umma - Tunji Alausa
  • Ministan Ma’adanai - Dele Alake
  • Ministan Yawon Buɗe-Ido - Lola Ade-John
  • Ministan Sufuri - Adegboyega Oyetola
  • Ministan Kasuwanci da Zuba Jari - Doris Anite
  • Ministan Wasanni - John Enoh
  • Ministan Abuja - Nyesom Wike
  • Ministar Al'adu - Hannatu Musawa
  • Ministan Tsaro - Muhammad Badaru
  • Ƙaramin Ministan Tsaro - Bello Matawalle
  • Ƙaramin Ministan Ilimi - Yusuf T. Sununu
  • Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane - Ahmed M. Dangiwa
  • Ƙaramin Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane - Abdullah T. Gwarzo
  • Ministan Kasafi da Tsare-Tsare - Atiku Bagudu
  • Ministan Muhalli (Kaduna)
  • Ƙaramar Ministar Abuja - Mairiga Mahmud
  • Ministan Albarkatun Ruwa - Bello M. Goronyo
  • Ministan Noma da Samar da Abinci - Abubakar Kyari
  • Ministan Ilimi - Tahir Maman
  • Ministan Harkokin Cikin Gida - Sa’Idu A. Alkali
  • Ministan Harkokin Waje - Yusuf M. Tuggar
  • Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a - Ali Pate
  • Ministan Harkokin 'Yan Sanda - Ibrahim Geidam
  • Ƙaramin Ministan Ƙarafa - U. Maigari Ahmadu
  • Ministan Ƙarafa - Shuaibu A. Audu
  • Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai - Muhammed IdrisMinistan
  • hari'a - Lateef Fagbemi
  • Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka - Simon B. Lalong
  • Ƙaramar Ministar Harkokin Cikin Gida - Imaan Sulaiman-Ibrahim
  • Ministan Ayyuka na Musamman - Zephaniah Jisalo
  • Ministan Albarkatun Ruwa - Joseph Utsev
  • Ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci - Aliyu Sabi Abdullahi
  • Ministan Kimiyya da Fasaha - Uche Nnaji
  • Ƙaramar Ministar Ƙwadago da Samar da Ayyuka - Nkiruka Onyejeocha
  • Ministar Harkokin Mata - Uju Kennedy
  • Ministan Ayyuka - David Umahi
  • Ministan Sufurin Jiragen Sama - Festus Keyamo
  • Ministan Matasa - Abubakar Momoh
  • Ministar Agajin Gaggawa da Rage Talauci - Betta Edu
  • Ƙaramin Ministan Albarkatun Iskar Gas -Ekperikpe Ekpo
  • Ƙaramin Ministan Man Fetur - Heineken Lokpobiri