Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Guardiola ya nemi ƴan wasa su taimaka wajen sauya halin da suke ciki
Pep Guardiola ya bukaci ƴan wasa da magoya bayan Manchester City su taimaka wajen sauya mawuyacin halin da ƙungiyar ta tsinci kanta bana.
City mai rike da Premier League na bara ta yi rashin nasara shida da canjaras ɗaya a karawa bakwai a jere a dukkan fafatawa a kakar nan.
Wasa ɗaya daga ciki ta tashi 3-3 da Fayenoord a Champions League, wadda ta fara cin uku, saura minti 15 a tashi aka zare su gabaki ɗaya suka tashi 3-3 a Etihad.
Wannan shi ne rashin ƙwazo mai muni a ƙungiyar tun bayan 2008, kuma rashin kokari a karon farko tun bayan da Pep Guardiola ya fara horar da tamaula.
City ta kara cin karo da koma baya, sakamakon da Liverpool ta doke ta 2-0 ranar Lahadi a gasar Premier League a Anfield.
Hakan ya sa ƙungiyar Etihad ta koma ta biyar ɗin teburi da tazarar maki 11 tsakaninta da Liverpool, mai jan ragama.
City na fatan kawo karshen rashin kokarinta ranar Laraba a wasan mako na 14 a Premier League da za ta karɓi bakuncin Nottingham Forest a Etihad.
City na fama da ƴan wasan da ke jinya ciki har da gwarzon Ballon d'Or, Rodri wanda ya gama buga wasannin kakar bana.
An kusa dawo da fara wasa da Kevin de Bruyne, wanda karo biyar ke canjin ɗan wasa, wanda ke farawa da zaman benci.
Ƙyaftin ɗin tawagar Belgium ya ji rauni tun a cikin watan Satumba, wanda ke fatan City za ta tsawaita masa ƙwantiragin ci gaba da takale da a ƙungiyar.
Har yanzu John Stones na jinya, wanda bai buga wasa biyu baya ba, Guardiola ya ce zai ci gaba da amfani da Stefan Ortega a gurbin tsare raga.
Wasu na cewa halin da City ke ciki watakila ta sayo ƴan wasa a watan Janairu, sai dai Guardiola ya ce zai ci gaba da amfani da waɗanda yake da su a kasa kawo yanzu.