Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace dama ta rage wa Ghana a wasannin neman zuwa Afcon 2025?
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Ghana na cikin zulumi game da yunƙurinta na samun gurbin shiga gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2025 a ƙasar Morocco.
Tawagar ta Black Stars ba ta ci wasa ko ɗaya ba a wasannin neman shiga gasar huɗu da ta buga a Rukunin F, wanda ya sa take a ƙasan teburi da maki biyu kacal.
An ci ta wasa biyu tare da yin canjaras biyu a rukunin da ya ƙunshi Angola ta ɗaya (maki 12), da Sudan ta biyu (maki 7), da Nijar ta uku (maki 4).
A yau Juma'a Black Stars za ta fafata da Angola a wasa na biyun ƙarshe a birnin Luanda na Angolan, wanda ya zama dole ta yi nasara idan har tana son samun gurbin.
Da a ce Nijar ba ta lallasa Sudan 4-0 ba ranar Alhamis, da tuni Ghanan ta samu tabbaci na gaza zuwa gasar da Morocco za ta karɓi baƙunci.
Amma yanzu idan ta samu nasara kan Angola, hakan zai sa ta kamo Nijar a yawan maki (7), sannan ya ƙara mata ƙwarin gwiwar tunkarar Nijar ɗin a wasan ƙarshe na rukunin - wanda shi ma dole ne sai ta ci shi.
Ghana ta kashe kofin Afcon sau huɗu a tarihi, amma ta kwana biyu ba ta yin wani abin kirki a gasar. Tun a zagayen rukuni ta koma gida a gasar ta 2023 da aka yi a Ivory Coast.
Sai dai kuma ita ce ta biyu a teburin Rukunin I na wasannin neman zuwa Kofin Duniya na 2026 da makinta tara - iri ɗaya da na Comoros da ke saman teburin - bayan wasa hurhuɗu.