Mahaukaciyar guguwa mai ruwa ta afka wa jihar Florida ta Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnan jihar Florida ya ce wata guguwa mai karfin gaske da ke tafiya da mamakon ruwan sama, da aka yi wa lakabi da suna Helene, ta afka wa a arewacin jihar ta Amurka.

Ron DeSantis ya ce tuni har ma ta yi sanadin mutuwar mutum daya, kuma ya yi gargadin cewa guguwar na tafiya da iskar da ke gudun sama da kilomita dari biyu a cikin sa’a daya, inda ya yi gargadin jama’a da su zauna da cikin gida.

Gwamnan jihar ta Florida ya ce mahaukaciyar guguwar, mai lakabin Helene, da ke tafe da gagarumin ruwan sama , wadda aka ayyana ta a matsayi na hudu a rukunin karfi ta sauka a arewacin jihar, ta Amurka, inda tuni ta janyo ajalin mutum daya, a sanadin wata alamar titi da ta fada masa.

Gwamnan ya yi gargadin cewa ruwan da guguwar ke antayowa ya kai na yadda zai iya shanye bene mai hawa biyu, da kuma iskar da ke tafiya da gudun kilomita 200 a cikin sa’a daya.

Ron DeSantis ya gargadi jama’a da su kasance a cikin gidajensu, inda babu hadarin guguwara yayin da wadanda ke cikin hadarin kuwa ake kwashe su zuwa wuraren da aka tanada na musamman har sai guguwar ta wuce;

Ya ce, ''za ta kasance gagarumar guguwa. Kuma yayin da take ratsawa ta arewacin Florida za ku ga yadda bishiyoyi za su rika faduwa. Wannan ita ce gaskiyar abin da muke gani a nan.’’

Gwamman na Florida ya kara da cewa hukumomi sun shirya tsaf domin fara aikin nema da ceto da zarar yanayin guguwar ya sassauta, babu hadari.

Ya ce tuni akwai jami’an aikin kar-ta-kwana na tarayya su dubu 35 da na jiha da kuma karin wasu zaratan ma’aikata na jihar da ke zaman jira yanayin ya sassauta su kama aikin, kawar da tarkace da sauran abubuwa da guguwa da ruwan suka jibge a tituna da hanya da sauran wurare.

Yayin da jihar ta Florida a Amurka ke fama da wannan guguwa ta Helene can kuwa a arewa da Akasar wata mahaukaciyar guguwar ce ita ma mai tafe da mamakon ruwan sama ita kuma wadda aka yi wa lakav bi da suna John ta afka wa tekun jihar Michoacan ta kasar Mexico, inda ta haddasa ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a yankuna gabar tekun