Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta dakatar da magoya baya 24 bayan samunsu da laifuka
Arsenal ta dakatar da magoya baya 24 daga shiga sitadiya kallon wasanninta.
Gunners ta same su da laifuka da yawa ciki har da kalaman wari da cin zarafi a filin Emirates da kafar sada zumunta.
Ta hana yan wasa 14 shiga Emirates kaka uku har da wasannin Premier League da za ta yi, yayin da 10 daga ciki aka dakatar da su kaka daya.
Yawancin mutanen sun aikata laifukan a filin wasa na Emirates da uku da aka same su da laifin a kafar sada zumunta.
Arsenal, wadda ta kare a mataki na biyu a teburin Premier League za ta fara wasan makon farko a kakar bana da karɓar baƙuncin Wolves a Emirates ranar 17 ga watan Agusta.