An raba maki tsakanin Aston Villa da Liverpool a Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Aston Villa da Liverpool sun tashi 2-2 a Prremier League da suka kara ranar Laraba a Villa Park.

Youri Tielemans da Ollie Watkins ne suka ci wa Villa ƙwallayen yayin da Liverpool ta zura biyu a raga ta hannun Mohamed Salah da Trent Alexander-Arnold.

A wasan farko da suka fuskanci juna a Anfield, Liverpool ce ta doke Villa 2-0 a Premier ranar 9 ga watan Nuwambar 2024

Da wannan sakamakon tazarar maki tsakanin Liverpool da Arsenal ya koma takwas, bayan da ƙungiyar Anfield ta yi wasa 26.

Aston Villa kuwa tana mataki na tara da maki 39, wadda ta yi nasara 10 da canjaras tara aka doke ta sau bakwai.

Arsenal ce a mataki na biyu a kan teburin Premier League da maki 58, yayin da Liverpool take da maki 61.

Tun farko cikin watan Maris ya kamata ƙungiyoyin su fafata a gasar, sai dai a lokacin Liverpool za ta fuskanci Newcastle United a wasan karshe a Carabao Cup a Wembley.

Ranar Lahadi 23 Liverpool za ta je Manchester City a Premier League, kwana uku tsakani ta karɓi bakuncin Newcastle United.

Ita kuwa Aston Villa za ta kara wasa a Villa Park da Chelsea ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu, kwana uku tsakani ta je Crystal Palace.