Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Atletico na zawarcin Partey, United na neman wanda zai maye gurbin Onana
Atletico Madrid na son ɗan wasan tsakiyan Arsenal Thomas Partey, mai shekara 31, wanda ta ke fatan ɗaukowa a bazara. (Marca)
Manchester United na da aƙalla masu tsaron raga hudu da ta ke Sanya wa ido, ciki har da golan Brighton Bart Verbruggen, mai shekara 22. (i paper)
Bournemouth ta fara cire rai kan riƙe ɗan wasan Sifaniya Dean Huijsen a kakar nan, sai dai ɗan wasan mai shekara 20, ya fi son komawa wani kulub a gasar Premier League maimakon komawa Bayern Munich ko Real Madrid. (Talksport)
Manchester United na sa ido kan mai tsaron ragar Southampton Aaron Ramsdale, mai shekara 26, gabannin damuwar da ake nunawa kan zaman dan wasan Kamaru Andre Onana, mai shekara 29. (The Sun)
Chelsea ma na bibiyar ɗan wasan gaba na Faransa mai taka leda a Brighton, Georginio Rutter mai shekara 22. (Florian Plettenberg)
West Ham kuwa zawarcin mai tsaron ragar Liverpool, wato Caoimhin Kelleher, mai shekara 26 ta ke yi, da fatan yin ram da shi da Zarar an buɗe kasuwar saye da saida ƴan wasa a lokacin bazara. (Daily Mirror)
Ɗan wasan gaba na Ipswich Town ɗan ƙasar Ingila Liam Deap, mai shekara 22, zai yi watsi da tayin komawa Manchester United a wannan bazarar mai zuwa.
Newcastle ta sha gaban Real Madrid da Barcelona a rububin ɗaukar matashin ɗan wasa Antonio Cordero mai shekara 18, wanda ke taka leda a Malaga. (Fabrizio Romano)
Aston Villa na samun ci gaba a tattaunawar da ta ke yi da Rosenborg, kan ɗan wasan tsakiya na Norway Sverre Halseth Nypan, mai shekara 8. (Sky Sports)
AC Milan da Roma na Shirin ƙulla yarjejeniyar musayar dan wasan Ingila Tammy Abraham, 27, da ɗan wasan tsakiya na Belgium Alexis Saelemaekers, 25, kan kwantiragin dindindin, a kaka mai zuwa. (Corriere dello Sport)
Kocin Newcastle Eddie Howe ya shaida wa hukumar kulob ɗin cewa yana son ya riƙe ƙwararrun ƴan wasan kungiyar a bazara, ciki har da ɗan wasan gaban Sweden Alexander Isak mai shekara 25, wanda ake alaƙanta shi da Liverpool da kuma Arsenal. (Teamtalk)
Tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp, wanda yanzu ya le riƙe da muƙamin shugaban kwallon kafa na duniya a Red Bull, ya bayyana a matsayin wanda zai iya maye gurbin Carlo Ancelotti a Real Madrid. (Sport)
Tottenham ta bayyana kocin Fulham Marco Silva da kocin Brentford Thomas Frank da kuma kocin Bournemouth Andoni Iraola a matsayin waɗanɗa ta ke nazarai don maye gurbin Ange Postecoglou idan har aka sallame shi. (Teamalk)
Akwai yiwuwar Iraola zai yi watsi da damar da za ta samu na komawa Tottenham domin ya ci gaba da zama a Bournemouth sakamakon Cherries na fafutukar fafatawa a gasar Europa League a kakar wasa mai zuwa. (Telegraph)