Champions League: Me kuke son sani kan wasan Real da Atletico

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid a wasan farko a zagayen ƴan 16 a Champions League ranar Talata a Santiago Bernabeu.
Atletico ta kawo wannan matakin ne, sakamakon da ta kare a mataki na biyar a teburin gasar zakarun Turai ta bana da aka sauyawa fasali.
Ita kuwa Real sai da ta buga karawar cike rukuni, bayan da ta yi ta 11 a teburin Champions League.
Real ɗin ta yi nasara a kan Manchester City da cin 3-2 a Etihad da kuma 3-1 a Bernabeu a wasa na biyu, kenan ta kai zagaye na biyu da cin 6-3 gida da waje.
Wannan shi ne karo na uku da za a kece raini tsakanin Real da Atletico a bana, bayan karawa biyu a gasar La Liga.
Spanish Liga ranar Asabar 8 ga watan Fabariarun 2025
- Real Madrid 1 - 1 Atletico Madrid
Spanish Primera Liga ranar Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024
- Atletico Madrid 1 - 1 Real Madrid
An hada ƙungiyoyin birnin Madrid karo huɗu a kaka 11 da suka gabata a Champions League, inda Real ta lashe kofin a 2014 da kuma a 2016 a kan Atletico.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai sun kara sau bakwai a tsakaninsu, inda Real Madrid ta yi nasara uku a Champions League da canjaras biyu, Atletico ta ci wasa biyu har da nasara 4-2 a European Super Cup a 2018/19.
Atletico ce ta biyu a teburin La Liga da maki 56 da tazarar maki ɗaya tsakani da Barcelona mai jan ragama kawo yanzu.
Real Madrid ta yi ƙasa zuwa mataki na uku a teburin La Liga da maki 54, bayan cin karawa 16 da canjaras shida aka doke ta wasa huɗu, bayan wasannin mako na 26.
Kylian Mbappe shi ne na biyu a cin ƙwallaye a La Liga mai 17 a raga, shi kuwa Julian Alvarez na Atletico yana mataki na tara mai ƙwallo 10 kawo yanzu.
Real Madrid sai ta kula da Alvarez, mai shekara 25 da sauran ƴan gaban Atletico, idan ba haka ba za su yi mata illa.
Alvarez ɗan wasan tawagar Argentina shi ne ya ci Athletic Bilbao ranar Asabar, wanda ya zura ƙwallo 21 a dukkan karawa tun bayan da ya koma Sifaniya daga Manchester City a watan Agustan bara.
Haka kuma Atletico Madrid ta anfana da cin ƙwallaye a daf da tashi a karawa a kakar nan.
Shin kun san Real ko Atletico na samun nasara idan ta haɗu da ƙungiyar Sifaniya a gasar zakarun Turai?
Wasa biyar Real ta yi rashin nasara a fafatawa 23 da cin 12 daga ciki da canjaras shida, ita kuwa Atletico ta ci tara daga karawa 21 da canjaras biyar da rashin nasara bakwai.
Real Madrid mai rike da Champions League tana da 15 jimilla, ita kuwa Atletico na fata.
Wasa tsakanin Real da Atletico a zakarun Turai
Kakar 2018/19
European Super Cup ranar Laraba 15 ga watan Agusta
- Real Madrid 2-4 Atletico Madrid
Kakar 2016/17
Champions League ranar Talata 2 ga watan Mayu
- Real Madrid 3-0 Atletico Madrid
Champions League ranar Laraba 10 ga watan Mayu
- Atletico Madrid 2-1 Real Madrid
Kakar 2015/16
Champions League ranar Asabar 28 ga watan Mayu
- Real Madrid 1-1 Atletico Madrid
Kakar 2014/15
Champions League ranar Talata 14 ga watan Afirilu
- Atletico Madrid 0-0 Real Madrid
Champions League ranar Laraba 22 ga watan Afirilu
- Real Madrid 1-0 Atletico Madrid
Kakar 2013/14
Champions League ranar Asabar 24 ga watan Mayu
- Real Madrid 4-1 Atletico Madrid
Ƴan wasan Real Madrid
Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Asencio.
Masu buga tsakiya: Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni da kuma Arda Güler.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.
Turpin ne zai busa wasan Real da Atletico

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta bayyana, Clement Turpin matsayin wanda zai yi rafli a wasan Real Madrid da Athletico Madrid a Champions League ranar Talata.
Real za ta karɓi bakuncin Atletico a wasan hamayya a zagayen farko na ƴan 16 a gasar ta zakarun Turai a Santiago Bernabeu.
Wannan shi ne karo na tara da alƙalin wasan ɗan kasar Faransa zai busa wasan da ya shafi Real Madrid a Champions League.
Cikin wasa takwas da Turpin ya yi rafli, Real Madrid ta yi nasara bakwai da canjaras ɗaya.
A wasan na ƴan birnin Madrid, an kara sau bakwai tsakanin Real da Atletico a gasar zakarun Turai shida da Europen Super Cup ɗaya.
Real ta yi nasara a Champions League uku da canjaras biyu, Atletico ta ci wasa biyu har da a European Super Cup da ta ci 4-2 ranar Laraba 15 ga watan Agusta 2018.
Wasannin da Turpin ya busa na Real Madrid:
Real Madrid 4-0 Ludogorets (2014/15 wasannin cikin rukuni)
Roma 0-2 Real Madrid (2018/19 wasannin cikin rukuni)
Real Madrid 3-2 Inter Milan (2020/21 wasannin cikin rukuni)
Chelsea 1-3 Real Madrid (2021/22 kwata fainal zagayen farko)
Liverpool 0-1 Real Madrid (2021/22 wasan ƙarshe)
Napoli 2-3 Real Madrid (2023/24 wasannin cikin rukuni)
Bayern Munich 2-2 Real Madrid (2023/24 daf da ƙarshe zagayen farko)
Manchester City 2-3 Real Madrid (2024/25 wasan cike gurbin shiga ƴan 16)










