Las Palmers ta je ta doke Barca mai bikin shekara 125 da kafuwa

Las Palmer

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Las Palmers ta je ta ci Barcelona 2-1 ta yiwa Barcelona fancale a makon da take bikin cika shekara 125 da kafuwa a tarihi.

Ƙungiyoyin sun tashi a minti 45 din farko ba ci, bayan da suka koma zagaye na biyu ne aka ci ƙwallayen.

Sandro Ramírez ne ya fara ci wa baki Ƙwallon farko daga baya Barcelona mai masukin baƘi ta farke ta hannun Raphinha.

To sai dai kuma Las Palmers ta kara na biyu ne a minti na shida tsakani da Barcelona ta farke a karawar ta La Liga mako na 15.

Da wannan sakamakon Las Palmers ta yi sama zuwa mataki na 14 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Watakila Real Madrid ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Barcelona ya koma ɗaya, idan ta yi nasara a kan Getafe ranar Lahadi.

Ranar Juma'a Barcelona ta cika shekara 125 a tarihi, sai gashi Las Palmers ta doke ta har gida, karon farko tun bayan Satumbar 1971, kuma ta yi wasa uku ba tare da nasara ba a lik.

Kawo yanzu Barcelona za ta buga wasa uku a waje a jere, biyu daga ciki a La Liga da kuma a Champions League.

Wasa uku da ke gaban Barcelona:

Spanish Liga Talata 3 ga watan Decembau

  • Mallorca da Barcelona

Spanish Liga Asabar 7 ga watan Disamba

  • Real Betis da Barcelona

Champions League Laraba 11 ga watan Disamba

  • Borussia Dortmund da Barcelona