Amorim zai fara aiki da United a tsakiyar watan Nuwamba

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sabon kocin da ake sa Manchester United za ta ɗauka Ruben Amorim zai ci gaba da zama a ƙungiyarsa ta Sporting har zuwa tsakiyar watan Nuwamba.

Babu cikakken bayani kan cewa ko an kammala cinikin Amorim da zai ci gaba da jan ragamar Old Trafford bayan korar Erik tan Hag da aka yi a ranar Litinin.

Daya daga cikin ɗan kwamitin amintattun United Sir Dave Brailsford ya shaida wa magoya baya cewa "an gama" lokacin da ya je kallon wasan da suka yi da Leicester har ya ɗauki hoto.

Ƙarin wata majiya daga Portugal ta tabbatar da wannan labari.

Amma jami'an Sporting sun yi shiru har yanzu ba su bayani ba kan ci gaba da yarjejeniyar.

Manchester United ta ƙi ta ce komai a kai.

Batu na baya-bayan nan shi ne cimma yarjejeniya kan kuɗaɗen da za a biya na tafiyar Amorim.

Sporting na son kocin ya zauna har bayan wasan da za su fafata da Estrela a ranar Juma'a.

Sporting za su buga wasan Champions da Manchester City a ranar Talata kuma su buga wasa da tsohuwar ƙungiyar Amorim Braga a Lig ranar 10 ga watan Nowamba, kafin a tafi hutun wasannin Nations Lig tsakanin 11 zuwa 19 ga watan Nuwambar.

Da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Juma'a ne ake sa ran Amorim ya yi tattaunawa da 'yan jarida gabanin wasan Estrela.

Awanni uku bayan nan shi ma Van NIstelrooy zai tattauna da manema labarai karon farko a matsayin kocin rikon kwarya.

Bayan nasarar da ya samu a wasan farko Nistelrooy ya ce zai ci gaba da aiki da Manchester United a "ko wanne irin mataki".

Unietd za ta yi wasa da Chelsea a ranar Lahadi a Premier ta yi da Leicester a ranar 10 ga watan Nuwamba.