Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Inter da Barcelona za su kai ruwa rana kan Fernandez, Arsenal na nazari kan Isak
Inter Milan da Barcelona na shirin zawarcin ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Argentina Enzo Fernandez, mai shekara 23, wanda a halin yanzu babu tabbas kan makomarsa a Stamford Bridge. (Sun)
Arsenal ta ayyana ɗan wasan gaban Newcastle Alexander Isak, mai shekara 25, a matsayin wanda ke kan gaba a jerin ƴan wasan da ta ke buƙata, kodayake Magpies za ta buƙaci a biya ta fam miliyan 100 kan ɗan wasan na Sweden. (Teamtalk)
Manchester United na zawarcin ɗan wasan gefe na Sporting Geovany Quenda, mai shekara 17, yayin da har ila yau ɗan wasan Portugal na ƴan ƙasa da shekara 21 kuma ya ke jan hanklalin Manchester City da Liverpool da Juventus. (Teamtalk),
Korarren kocin Manchester United Erik ten Hag bai so siyan ɗan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee daga Bologna a bazara ba kuma ya fusata lokacin da dan wasan da aka saya kan farashin fam miliyan 36.5 ya zo Old Trafford da ƙiba. (Sun)
Tottenham na sha'awar ɗan wasan tsakiyan Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, amma ba sa tunanin za su iya ɓamɓare shi daga AC Milan a watan Janairu. (Football Insider ).
Chelsea ba za ta yi tunanin sayar da ɗan wasan baya Benoit Badiashile, mai shekara 23 ba, yayinda ta ke shirin ci gaba da riƙe ɗan wasan na Faransa na dogon lokaci. (Fabrizio Romano)
Nottingham Forest na son daukar ɗan wasan Bayern Munich Mathys Tel, mai shekara 19, a matsayin aro amma ɗan wasan na Faransa na kasa da shekara 21 ba shi da shirin barin Bavaria a wannan hunturun. (Sky Germany)
Tsohon kociyan Chelsea da Everton, Frank Lampard, ya bayyana a matsayin ɗan takarar karɓar ragamar aiki daga kociyan AS Roma Ivan Juric, idan har ƙungiyar ta yanke shawarar rabuwa da kocin ɗan ƙasar Croatia. (Gazzetta dello Sport)
Tottenham za ta fara nazarin ƙara shekara guda kan kwantiragin ɗan wasan gaban Koriya ta Kudu Son Heung-min, mai shekara 32. (Telegraph)
Manchester United za ta tattauna da sabon kocinta Ruben Amorim kafin yanke shawara kan kwantaragin ƴan wasan da ke gab da kammala kwantiraginsu. (ESPN).
Aston Villa na dab da kulla sabuwar yarjejeniya mai tsoka da ɗan wasan gaban Ingila Morgan Rogers, mai shekara 22. (Football Insider)