Espen Eskas ne zai busa wasan Real da Brest a Champions League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta bayyana Espen Eskas a matakin wanda zai yi rafli a wasan Real Madrid da Brest a Champions League ranar Laraba.

Ƙungiyar Sifaniya za ta ziyarci Brest ta Faransa a Stade du Roudourou, domin buga wasan karshe a cikin rukuni a kakar nan.

Wannan shi ne karo na biyu da raflin ɗan kasar Norway zai yi alkalancin wasan Real Madrid a gasar zakarun Turai.

Ya fara busa fafatawar da Real Madrid ta yi nasara 1-0 a kan Union Berlin a karawar cikin rukuni a kakar 2023/24.

Real Madrid tana mataki na 16 a teburi da maki 12, bayan cin wasa huɗu da canjaras uku.

Ita kuwa Brest tana ta 13 a teburi da maki 13, bayan cin karawa huɗu da canjaras ɗaya aka doke ta wasa biyu.

Wasannin da za a buga ranar Laraba a Champions League.

  • Aston Villa da Celtic
  • Barcelona da Atalanta
  • Bayer Leverkusen da Sparta Prague
  • Bayern Munich da Slovan Bratislava
  • Borussia Dortmund da Shakhtar Donetsk
  • Brest da Real Madrid
  • Dinamo Zagreb da AC Milan
  • Girona da Arsenal
  • Inter Milan da Monaco
  • Juventus da Benfica
  • Lille da Feyenoord
  • Manchester City da Club Brugge
  • PSV da Liverpool
  • Red Bull Salzburg da Atlético Madrid
  • Sporting da Bologna
  • Sturm Graz da RB Leipzig
  • Stuttgart da PSG
  • Young Boys da Red Star Belgrade