Espen Eskas ne zai busa wasan Real da Brest a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta bayyana Espen Eskas a matakin wanda zai yi rafli a wasan Real Madrid da Brest a Champions League ranar Laraba.
Ƙungiyar Sifaniya za ta ziyarci Brest ta Faransa a Stade du Roudourou, domin buga wasan karshe a cikin rukuni a kakar nan.
Wannan shi ne karo na biyu da raflin ɗan kasar Norway zai yi alkalancin wasan Real Madrid a gasar zakarun Turai.
Ya fara busa fafatawar da Real Madrid ta yi nasara 1-0 a kan Union Berlin a karawar cikin rukuni a kakar 2023/24.
Real Madrid tana mataki na 16 a teburi da maki 12, bayan cin wasa huɗu da canjaras uku.
Ita kuwa Brest tana ta 13 a teburi da maki 13, bayan cin karawa huɗu da canjaras ɗaya aka doke ta wasa biyu.
Wasannin da za a buga ranar Laraba a Champions League.
- Aston Villa da Celtic
- Barcelona da Atalanta
- Bayer Leverkusen da Sparta Prague
- Bayern Munich da Slovan Bratislava
- Borussia Dortmund da Shakhtar Donetsk
- Brest da Real Madrid
- Dinamo Zagreb da AC Milan
- Girona da Arsenal
- Inter Milan da Monaco
- Juventus da Benfica
- Lille da Feyenoord
- Manchester City da Club Brugge
- PSV da Liverpool
- Red Bull Salzburg da Atlético Madrid
- Sporting da Bologna
- Sturm Graz da RB Leipzig
- Stuttgart da PSG
- Young Boys da Red Star Belgrade







