Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wolves na fatan jin daɗi na dindindin a nan gaba
"Muna da kyan da za mu ci gaba da zama a Premier, kuma za mu zauna," in ji sabon kocin Wolves Gary O'Neil da ya sha kashi a hannun Man City da 2-1 a ƙarshen lokaci.
Kocin ya yi amannar cewa Wolves za ta bar matsayin da take a yanzu a ƙarshen teburin Premier bayan wasa takwas da ta buga inda ta samu maki guda.
Rashin nasarar ta zo ne bayan na'uarar VAR da ke taimakawa alƙalin wasa ta ce babu satar gida a kwallon da John Sone ya ci a ƙarshen lokaci.
Wannan ya tabbatar da nasarar City tare da barin O'Neil da jin cewa ana nuna banbanci tsakanin manyan ƙungiyoyi da ƙanana a gasar.
Ya nutsu tare da kaucewa sukar jami'ai, amma fusatar hukuncin VAR ta sa Wolves ta ci gaba da neman a watsar da fasahar da aka kawo cikin kwallo baki ɗaya.
Yanzu Wolves za ta sake karawa da Brighton a ranar Asabar - inda jadawalin ya nuna za ta kara da kungiyoyi bakwai na saman Premier cikin wasa tara da za ta yi na bana.
Su ne za su fi buga wasa masu zafi a wannan kakar sama da kowacce ƙungiya - kamar yadda kamfanin Opta mai fitar da ƙididdiga ya bayyana, yayin da suke da maki ɗaya na canjaras da suka yi 1-1 da Nothengham Forest.
Amma rawar da take takawa ba wadda za a yi farin ciki da ita ba ce. Amma Wolves na kammala wa lafiya a mafi yawan wasanninta.